✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Budurwa ta hallaka kanta saboda hana ta saurayin da take so

Wata budurwa mai shekara 20 mai suna Gambo Jibirin Gambara da ke karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, ta kwankwadi maganin kwari inda ta…

Wata budurwa mai shekara 20 mai suna Gambo Jibirin Gambara da ke karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, ta kwankwadi maganin kwari inda ta hallaka kanta saboda iyayenta sun hana ta saurayin da take so ta aura. Lamarin wanda ya sa iyayen Gambo garzayawa da ita Babban Asibitin Birnin Kudu domin ceton ranta, amma kafin likitoci su yi komai ta cika. Kakakin Rudunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, SP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce samun labarin ke da wuya suka tura jami’ansu zuwa asibitin domin ganin an taimaka wajen ceto rayuwarta, sannan su yi kokarin samun wasu kalamai daga bakin yarinyar, amma hakan samu ba. Ya ce ko da zuwansu ta riga ta mutu. Jinjiri ya kara da cewa jami’ansu na bin diddigin lamarin don gano asalin yadda yarinyar ta kai ga rasa ranta.