✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bude makarantu: Muna duba yiwuwar karkasa azuzuwa — Gwamnati

Gwamnatin Tarayya na shirin fitar da sabbin tsare-tsaren da za su tabbatar da bude makarantu a kasar nan. Gwamnatin na duba yiwuwar karkasa azuzuwa da…

Gwamnatin Tarayya na shirin fitar da sabbin tsare-tsaren da za su tabbatar da bude makarantu a kasar nan.

Gwamnatin na duba yiwuwar karkasa azuzuwa da fidda sabbin tsare-tsaren gudanar da karatu a dukkan matakai kafin ba da umurnin bude makarantun.

Karamin Ministan Ilimi Emeka Nwajiuba ya bayyana haka a lokacin jawabin kwamitin ko-ta-kwana da ke yaki da cutar coronavirus.

Nwajiuba ya karyata ji-ta-ji-ta da da yawo a shafukan zumunta cewa gwamnatin tarayya za ta bude makarantu a ranar 8 ga watan Yuni.

Ya ce duk da muhimmancin da makarantun da kuma bukatar bude su, gwamnati ba za ta bude su ba har sai ta tabbatar za a iya kiyaye lafiyar dalibai.

“Sai mun tabbata dukkan dalibai na iya zuwa makaranta su dawo ba tare harbuwa da cutar ba.

“Idan har ba mu tabbatar da hakan ba, to za mu iya jefa su cikin hadari saboda gaggawarmu.

“Ba za mu iya dawo da abun da muka rasa ba,” inji Ministan.

Ministan ya bukaci makarantun kudi su ba wa gwamnati hadin kai domin tabbatuwar tsare-tsaren bude makarantun.

“Muna duba yiwuwar karkasa azuzuwa zuwa safe da rana kuma za mu karkasa kayayyakin koyarwa saboda zu isa yadda ake bukata.

“Ba na tunanin za mu shirya azuzuwan dare, amma za mu iya amfani da azuzuwan safe da rana kafin nan” inji shi.

A ‘yan kwanakin nan ne dai Kungiyar Masu Makarantu Masu Zaman Kansu (APSON) ta bukaci gwamanti ta taimaka musu da basussuka saboda farfadowa daga halin da suka shiga da kuma ceto su daga durkushewa.