✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Brown Ideye ya lashe gasar firimiya a karon farko

dan kwallon Najeriya da yanzu haka yake buga wa kulob din Olympiacos na Greece kwallo Brown Ideye ya samu nasarar lashe gasar rukuni-rukuni na kasar…

dan kwallon Najeriya da yanzu haka yake buga wa kulob din Olympiacos na Greece kwallo Brown Ideye ya samu nasarar lashe gasar rukuni-rukuni na kasar Girka da ake kira Super League a karon farko a tarihin kwallonsa.
dan kwallon ya samu nasarar haka ne a ranar Lahadin da ta wuce bayan kulob dinsa na Olympiacos ya lallasa na AELKalloni da ci 5-1 kuma Ideye yana daga cikin ’yan kwallon da suka zura kwallo a raga a lokacin wasan.
dan shekarar 27, tsohon dan kwallon West Brom da ke Ingila tuni ya bayyana farin cikinsa a kan wannan nasara da ya samu a kafar sadarwasa ta Twitter.  “Ina matukar mika godiyata ga magoya bayana musamman wadanda suka kasance tare da ni har na kawo wannan matsayi.  Yanzu haka mun zama zakara a gasar rukunin Girka’.
Brown Ideye ya buga wa kulob din wasanni 24 a bana inda ya samu nasarar zura kwallaye 10 a raga.
Idan za a tuna Brown Ideye yana daga cikin \yan kwallon Super Eagles da suka lashe wa Najeriya kofin Afirka a shekarar 2013 a karkashin tsohon koci  Stephen Keshi. Sannan ya taba buga wa kulob din Dynamo Kiebe na Rasha kwallo.