✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Brazil ta yi zaman makoki saboda mutuwar ’yan kwallonta

Tun bayan aukuwar hatsarin jirgin sama da ya yi sanadiyyar mutuwar ’yan kwallon kulob din Chapecoense na Brazil tare da jami’ansu, a ranar Litinin da…

Tun bayan aukuwar hatsarin jirgin sama da ya yi sanadiyyar mutuwar ’yan kwallon kulob din Chapecoense na Brazil tare da jami’ansu, a ranar Litinin da ta gabata sai kasar ta bayar da sanarwar yin zaman makoki na kwana uku zuwa jiya Alhamis don nuna alhini a kan rasuwar ’yan kwallon.
Wani jirgin sama mai dauke da mutum 81, ciki har da ’yan kwallon kafa na kulob din Chapecoense na Brazil, ya fadi a kusa da birnin Medellin na kasar Kolombiya a ranar Litinin da ta gabata inda ya yi sanadiyyar rasuwar fiye da mutum 75 da ke cikin jirgin yayin da shida daga ciki sun samu mummunan rauni kuma yanzu haka suna asibiti ana yi musu magani.
Rahotanni sun ce akalla mutum shida ne suka tsira kuma jirgin  ya samu matsalar na’ura ce a lokacin da yake tafiya a sama, al’amarin da ta sa ya fado ba tare da shiri ba.
Jami’an filin saukar jiragen sama sun ce jirgin, wanda aka dauki hayarsa, ya taso ne daga Bolibia yana dauke da tawagar ‘yan kwallon kulob din Chapecoense da jami’ansu da ’yan jarida da kuma wasu fasinjoji.
Tawagar ’yan kwallon na shirin karawa ne a wasan karshe na Copa Sudamericana tare da kungiyar Atletico Nacional na birnin Medellin a shekaranjiya Laraba sai wannan hatsari ya rutsa da su inda daukacin ’yan kwallon suka rasu da hakan ta sa aka dage wasan.
Ya zuwa shekaranjiya Laraba kulob din Atletico Nacional ya umarni hukumar da ke kula da gasar da ta bai wa kulob din Chapeecoense kofin a matsayin girmamawa duk da yake ba su buga wasan ba.  Haka kuma kulob da dama a Brazil sun nuna za su yi karo-karo wajen ba kulob din ’yan kwallo a kakar wasa mai zuwa don nuna alhini ga abin da ya samu ’yan kwallon kulob din.
Shararrun ’yan kwallo irin su Pele da Diego Maradona da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da Neymar tuni suka aika sakonnin ta’aziyyarsu ga Hukumar kwallon kafa ta Brazil a kan wannan rashi da aka yi.  Ita ma Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya FIFA tuni ta aika nata sakon ta’aziyyar game da rasuwar ’yan kwallon.f