✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Brazil ce za ta lashe kofin duniya a bana – Pele

Shahararren dan kwallon duniya Pele a ranar Litinin da ta gabata ne ya nuna kasar haihuwarsa Brazil ce za ta lashe kofin kwallon kafa na…

Shahararren dan kwallon duniya Pele a ranar Litinin da ta gabata ne ya nuna kasar haihuwarsa Brazil ce za ta lashe kofin kwallon kafa na duniya a bana wanda za a yi a Rasha a watan Yuni.

Pele ya ce idan aka yi la’akari da yadda kasar Brazil ta hada zaratan ’yan kwallo a bana, ba ya shakkar akwai wata kasar da za ta iya taka wa Brazil burki a gasar cin kofin duniya na bana.

Pele ya ce, yakamata a jinjina wa kocin Brazil na yanzu Tite don ya yi nasarar hada zaratan ’yan kwallon da za su iya tunkarar kowace kasa a gasar cin kofin duniya.

Idan za a tuna kasar Jamus ce ta lallasa Brazil da ci 7-1 a gasar cin kofin duniya a shekarar 2014 a matakin kusa da na karshe (semi-fainal) duk da cewa kasar ce ta dauki nauyin gasar.

Brazil dai tana takama da zaratan ’yan kwallo ne ciki har da dan kwallon da ya fi tsada a duniya Neymar da yanzu haka yake kwallo a kulob din PSG na Faransa.