✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Brahim Diaz ya koma Madrid bayan zaman aro a Milan

Real Madrid ta dauki Brahim a Janairun 2019 daga Manchester City.

Real Madrid ta yi wa dan wasanta Brahim Diaz kiranye bayan kaka uku yana zaman aro a kungiyar AC Milan da ke Italiya.

Diaz mai shekara 23, ya lashe kofin Serie A tare da Milan a 2021/21, sannan ya buga wasan daf da karshe a Gasar Zakarun Turai wato Champions League a bana, inda Inter Milan ta fitar da su.

Real Madrid ta dauki Brahim a Janairun 2019 daga Manchester City, wanda ya dauki kofin La Liga a Santiago Bernabeu a kakar 2019/20 da Spanish Super Cup a 2020.

An bayar da shi aro ga AC Milan a cikin Satumbar 2020, inda ya yi kaka uku tare da cin kwallo 18 a dukkan fafatawar da ya yi wa Milan.

Ya fara taka leda a matashin dan wasa a Malaga, daga nan ya koma Manchester City, ya fara taka leda a Ingila a karawa da Swansea a EFL Cup a 2016/17 yana da shekara 17.

A kakar 2017/18 ya fara buga Premier League da FA Cup, wanda ya bayar da gudunmuwar da City ta lashe lik da League Cup.

Haka kuma ya dauki Community Shield a dai Manchester City.