Gwamnatin jihar Borno ta dan sassauta dokar hana fita domin bai wa masu wasu sana’o’i dama su biya bukatar masu azumin watan Ramadan.
Sassaucin dai ya ba masu kosai, da waina, da shayi, da ruwan sanyi damar sayarwa ga jama’a masu azumi tun daga karfe 4 na yamma.
Sakataren kwamitin hana yaduwar cutar coronavirus, Kwamishinan Lafiya Dr Salisu Kwayabura ne ya sanar da hakan.
- Azumin kulle: Yadda wasu mutanen Borno suka ‘yi sahur da ruwa’
- COVID-19: An killace mutum 99 a Borno
Ya ce an yi wannan sassauci ne domin a bai wa Musulmi damar samun abin bude baki, mussaman ma wadanda ba su da halin dafawa a gidajensu.
A wata dabam kuma gwamnatin ta jihar Borno ta fara rabon kayan abinci ga jama’a ranar Asabar.
Gwamna Babagana Zulum ne ya kaddamar da rabon abinci a sansanin ’yan gudun hijira da ke Muna.
Gwamnan ya yaba wa jama’a saboda hadin kan da suka bayar wajen yin biyayya ga dokar kullen da aka ayyana, sannan ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya kamata don saukaka wa jama’a halin da suke ciki.
Ya kuma ce daga ranar Litinin za a dan sarara kadan na ’yan sa’o’i domin bai wa jama’a damar fita su sayi abubuwan bukata.
Gwamna ya kuma gode wa Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas saboda tallafin kayan abinci ta bayar da ya kai buhun shinkafa 1,500 da gero 1,500 da sauransu.
Kwana guda kafin fara azumin watan Ramadana ne dai dokar kulle ta tsawon mako biyu da gwamnatin jihar Borno ta ayyana ta fara aiki, lamarin da ya sa mutane da dama kokawa saboda rashin samun abin da za su sha ruwa da shi.
Gwamnatin dai ta kafa dokar da nufin hana cutar coronavirus yaduwa a jihar.