✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boren matan sojoji

Kimanin mako biyu da suka gabata, wani rukuni na mata sun shiga garin Maiduguri don yin zanga-zanga kan tura mazajensu sojoji zuwa fagen daga don…

Kimanin mako biyu da suka gabata, wani rukuni na mata sun shiga garin Maiduguri don yin zanga-zanga kan tura mazajensu sojoji zuwa fagen daga don fafatawa da kungiyar Boko Haram.
Matan su kimanin 100, sun jawo tsaiko a kofar shiga Birged na 21 na sojojin tankokin yaki da ke barikin Giwa da ke fadar Jihar Borno. Sun ce ba su amince a tura mazajensu zuwa Damboa da sauran garuruwa da rahotanni suka ce mahara sun kwace ba. Matan, wadanda matakin da suka dauka ya takaita shiga da fita a cikin bariki, sun tsaya kai da fata cewa fuskantar maharan da irin makaman da ake ba sojojin, tamkar tura su su je su kashe kawunansu ne. Irin wannan bore ya faru kwana daya kafin wannan a Barikin Maimalari inda wasu matan suka yi zanga-zanga.
Zanga-zangar da ba a saba ba da yadda ta taro manema labarai, ba ta girgiza mahukuntan soja ba, wadanda suka fitar da gargadi mai kaushi. Abin da ke gaban soja a lokacin yaki shi ne kasarsa ba tunanin mata ko iyalinsa ba. Kuma cikin nauyin da ke kansa akwai kare kasa daga harin cikin gida da barazanar waje. Kuma jawo hankalin jama’a da matan suka yi ta hanyar zanga-zanga ba zai yi tasiri ga dabi’un sojojin a irin wannan lokaci ba, da miyagun hare-haren suka gagari duk yunkurin da ake yi don dakile su.
Aikin tura sojoji zuwa fagen daga ko aiki, abu ne da ya shafi hukumomin soja kadai, kuma bai kamata matansu ko wani mutum da ke wajen aikin soja ya tsoma baki ba. Don haka wajibi ne matan su fahimci hakikanin lamarin ta yadda za su kauce wa tsoma baki kan tura mazajensu wurin aiki, kuma su guji yin duk abin da zai kara lalata harkokin tsaro a garin Maiduguri da kewayensa. Mafi karancin abin da za su yi a irin wannan hali shi ne su goyi baya tare da karfafa wa mazajensu a daidai lokacin da suke mika duk wani korafi ta hanyoyin da suka kamata, kamar kungiyar Matan Manyan Sojoji don isarwa ga hukumomin da suka dace.
Zanga-zangar matan ta dada nuna damuwar da ake nunawa ciki har da ta manyan jami’ai da wasu sojojin kansu cewa ba a ba sojojin da ke zuwa fagen daga isassun kayan aikin da za su iya fuskantar abokan gaba.
Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima, ya taba kukan cewa ’yan ta’adda sun fi sojojin da suke fafatawa da su makamai. Kuma tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako ya yi irin wannan kuka. Kuma duk da cewa mahukuntan soja sun rika musanta cewa ba sub a jami’ansu isassun makamai, kuma yadda akai-akai maharani ke kai munanan hare-harensu ba tare da fuskantar kalubale ba ya nuna da walakin. Sojoji da dama sun rasa rayukansu a fafatawa da maharani.
karuwar irin wannan damuwa da lura da yadda ake samun rahotannin sojoji na gudu daga aiki, wajibi ne gwamnati da mahukuntan soja su hanzarta samar da wadatattun makamai a yankunan da ake fafatawa. Barzanar za a kori matan da suka yin zanga-zanga daga bariki ba mafari ne na magance batutuwan da suka tabo ba. A matsayinsu na yadda suke ganin yadda takwarorinsu ke zama zawarawa na iya sanya su a cikin damuwar da za ta sa su bayyana kukansu domin a ji. Yayin bayyana damuwarsu game da makomarsu, wasu daga cikinsu sun yi zargin cewa takwarorinsu da suka rasa mazajensu ‘an yi watsi da su,’ bayan mutuwar mazajen a fafatawa da mayakan Boko Haram.
Rashin ingantattu kuma wadatattun makamai ga rundunar soja na iya karya kwarin gwiwan sojoji, kuma haka na iya jawo matsala; wannan ne abin da mahukuntan soja ya wajaba su zage dantse don kauce masa. Idan dimbin kudin da ake warewa ga harka tsaro za a yi amfani da su yadda ya kamata, kasar nan za ta iya ganin baya ko akalla ta dakile ayyukan maharani zuwa yanzu. Kuma domin karfafa wa maza da matanmu da ke sanye da kaki da aka tura fagen daga ko wurin da ke da hadari, iyalan da suka rasa mazajensu ta wajen kwantawa dama a fagen daga don kare martabar kasar nan, ya wajaba a kula da su yadda ya kamata. Wannan ne wurin da kwamitin T. Y. danjuma da aka kafa don tallafa wa wadanda hare-haren Boko Haram ya tagayyara za taka muhimmiyar rawa wajen magance tsoron da matan suka nuna.