Wasu abubuwan fashewa da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa, sun kashe kimanin mutane 26, ciki har da mata da ƙananan yara a kusa da garin Rann da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno.
Majiyoyin tsaro da na cikin gari sun bayyana cewa mutane da dama sun jikkata bayan da motar da ke ɗauke da wadanda abin ya shafa zuwa Gambarou Ngala ta taka abin fashewar.
Wata majiya ta ce, “Ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma rahotanni na farko sun nuna cewa mata huɗu da yara shida da maza 16 ne suka mutu a wannan fashewar.”
Ta ci gaba da cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Furunduma, kimanin kilomita 11 daga garin Rann, da misalin karfe 11 na safe a ranar Litinin.
- Mutanen da talauci ya yi wa katutu zai ƙaru a Nijeriya — Bankin Duniya
- NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya
Ta ƙara da cewa an kai wasu da suka jikkata asibitin Rann domin kula da su.
Babu wata sanarwa a hukumance daga bangaren sojoji ko ’yan sanda game da faruwar lamarin.
Sai dai kuma, kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Borno, Kenneth Daso, bai yiwu ba saboda layin wayarsa ba ya shiga.