Kimanin yara guda biyar sun rasa rayukansu a sakamakon wasu ababen fashewa da suka tarwatse a wurare biyu a birnin Herat na Afghanistan.
Rahotannin da DW ta samu na cewa akwai wasu mutane 20 da ababen fashewar suka jikkata.
- Yadda rashin wutar lantarki ke ruguza kasuwanci a Najeriya
- Za mu kawo sojojin haya daga ketare idan Buhari ya gaza magance ta’addanci —El-Rufai
Hukumomin Taliban masu mulkin Afghanistan sun ce lamarin ya faru ne a ranar Jumma’a, lokacin da kananan yara suka tono ababen fashewar, suka fara wasa da su.
Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin tayar da bama-baman.
Sai dai Taliban ta ce ta yi nasarar tono wasu karin bama-bamai guda biyu da ba su kai ga fashewa ba a kusa da wurin da lamarin ya faru a ranar Jumma’a.