✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bolar bayan gidan sarki da yadda take jefa Kanawa a cikin kunci

Jihar Kano kadai na tara shara tan 96,000 a kowace shekara.

Mazauna Unguwar Durumin Iya da ke Karamar Hukumar Birnin Kano kan shiga cikin kunci da damuwa kan yadda bolar da ke jikin gidan Sarkin Kano da ake yi wa lakabi da ‘Bolar Bayan Gidan Sarki’ ke saurin taruwa kuma ba a kwashe ta a kan lokaci.

Wakiliyarmu wadda ta ziyarci bolar a karo na farko ta ruwaito cewa ta iske bolar ta tumbatsa har kan titi, kuma hakan ya sanya rara-gefe masu ababen hawa suke bi a titin da ke kan hanyar, wanda hakan yake haifar da cinkoso a yankin.

Kazalika daliban Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Hasiya Bayero da ke makwabtaka da bolar da malamansu sukan koka da yadda cinkoson ke kawo tsaiko gare su musamman ga wadanda sai sun ketare titi ko hawa mota kafin su je gidajensu.

Bolar shara ce da unguwanni da dama da ke kewayen yankin suke kawowa, wanda hakan ya sa ba ta cika mako take tumbatsa, ta kwarara har cikin makarantar ’yan matan da magudanun ruwa da gidajen da suke makwabtaka da ita.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa hakan ya sa hukumar makarantar take neman juyar da kofar makarantar daga inda take a yanzu domin kauce wa barazanar da wannan shara take mata kafin hukuma ta kwashe ta.

Abin da daliban makaranta da mazauna unguwar ke cewa

Wani mai suna Halliru Musa ya ce duk lokacin da ya zo zubar da sharar gidansa yakan ji takaicin cikarta, amma kasancewar ba yadda zai yi dole ya zuba a haka.

Ita kuwa Hajiya Zuwaira ta ce warin sharar na hana ta sukuni a cikin gidanta, kuma iska kan kwaso sharar ta dawo da ita cikin gidajen da suke kewayen sharar, kuma dadin dadawa tana kawo sauro da beraye.

Daliban Sakandaren ’Yan Mata ta Hasiya Bayero da Aminiya ta tattauna da su kuma suka nemi a sakaya sunansu, kan yadda sharar take takura musu, daya daga ciki ta ce; takan shiga fargaba idan hadari ya taso, domin hakan na nufin tafiya ta cikin jagwalgwalon bolar da kuma kwata, wadanda suke bata masu kayan makaranta.

Wata dalibar cewa ta yi: “Warin sharar na damunmu a makaranta, kuma ba yadda za mu yi, kuma ko an yi shara sai ka ga ledoji har cikin ajujuwanmu.”

Wani mai gudanar da sana’a a tsallaken bolar ya ce tana haddasa musu beraye da sauro, ban da warinta da ke cutar da su.

“Ina kira ga gwamnati ta duba ta kawo mana agaji kan wannan shara, idan ma kara wajen zubar da sharar za a yi ko a sauya mata wuri saboda dalibai mu dai a yi a taimaka mana,” inji shi.

Tarihin ‘Bolar Sarki’

Mai Unguwar Durumin Iya, Alhaji Jamilu Bahago, ya bayyana tarihin fara zuba shara a wurin har ta kai ga yin sunan da unguwannin kusa suke zuwa zuba shararsu.

Ya ce tarihinta ya soma ne tun lokacin da wurin yake kududdufi, daga bisani aka fara binne mamata, wato kusan shekara 60 da suka gabata, kafin daga bisani ta dawo Bolar Kurmawa.

“Akwai lokacin da mutane ma suka maida ta gun bahaya da fitsari, har sai da marigayi Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya sa aka gina gidan wanka da bahaya, don kauce wa bahaya a bainar jama’a.”

“Rashin kwashe sharar a kan lokaci ya dade yana damun mu kuma mun sha kai kokenmu a rubuce ga na gaba da mu a masarauta.

“Sannan ita kanta gwamnati musamman kamfanin da aka dora wa alhakin kwashe sharar na da masaniya kan hakan,” inji Mai Unguwar.

Ya ce, “Mun zauna mun yi magana da Kamfanin Capegate kan sharar har suka ce za su ware mutum biyu daga al’ummar unguwar su rika biyan su Naira dubu 30 da kayan aikin da za su rika tabbatar da an zuba sharar a inda ya dace da kuma tattara ta kafin ma’aikata su zo kwashe ta idan ta cika.

“To sai dai har yanzu fa ba ni da labarin an yi haka ko ba a yi ba domin kuwa ba su sake tuntubata ba, ni kuma na kira su a waya amma shiru kake ji.

“Muna kira ga gwamnati ta taimaka ta kara mana cibiyoyin zuba shara da kuma kwashe ta a kan lokaci, domin kuwa ita kadai ce shara a kewayen Birni da ake mata lodi tun safe har dare wani lokacin ma a mota daga makwabtan unguwanni irin su Jakara da Gwazaye da Soron Dinki da sauransu,” inji shi.

Ya ce a baya gwamnatin na debe ta a kan loakci, yanzu ne abin ya munana, domin wani lokacin madadin a kwashe ta sai dai hukumar da ke da alhakin kwashewar ta tattara ta a matsar da ita gefe, ko idan hakan bai samu ba al’ummar unguwar su matsar da ita da kansu domin samun hanyar wucewa.

Abin da gwamnati da fada suka ce

Da Aminiya ta tuntubi Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Kano, mai magana da yawaunta, Sunusi A. Kofar Na’isa ya ce hukumar na iya kokarinta wajen kwashe sharar, musamman a karkashin sabon tsarin da ta bullo da shi a baya-bayan nan na tsaftace Jihar Kano.

“Duk inda shara take ma’aikatanmu na zagaye idan sun ga ta cika su kwashe, idan kuma an samu ta cika idonsu bai kai ba, a sanar da ofishinnu mafi kusa za mu kwashe ta,” inji shi.

Kamfanin da Gwamnatin Jihar Kano ta dora wa alhakin kwashe sharar wato Capegate ta bakin Shugaban Gudanarwarsa, Alhaji Bello Abba Yakasai, ya ce tsadar man dizel da motocin kwashe sharar ke amfani da shi da kuma al’umma da ba sa biyan kudin kwashe sharar, ke kawo musu tsaiko kuma hakan bai hana kamfanin kwashe ta ba.

Muna sane da bolar —Masarautar Kano

Alhaji Abba Yusuf Danmakwayo shi ne Sakataren Masarautar Kano, da Aminiya ta tuntube shi kan sharar la’akari a makwabtakarta da gidan Sarkin, ya ce Masarautar Kano na sane da ita, kuma tana shawartar al’ummar yankin da su rika kai kokensu ga dagatai da hakimansu idan irin haka ta faru domin daukar matakin da ya dace.

Ya ce idan har abin ya fi karfin dagatai da hakiman to masarautar za ta shiga domin mika koken ga hukumomin da abin ya shafa kai-tsaye.

“Muna iyakar kokarinmu domin ganin mu da kuma dagatai da hakimai mun shige gaba domin share wa talakawanmu hawaye a al’amuran da suke damun su, haka ne ya sa muke shawartar su da sanin hukumonin da matsalar ta shafa domin magance su a koyaushe,” inji shi.

Matsalar cikowar bola a Kano ba sabuwar aba ba ce, domin a 2021 Hukumar REMASAB da a baya ke da alhakin kwashe sharar, ta ba da sanarwar cewa jihar kadai na tara shara tan 96,000 a kowace shekara.

Wannan ne ya sa a watan Satumban 2021 Gwamnatin Jihar Kano ta yi hadin gwiwa da Kamfanin Kwashe Shara na Capegate don kwashe sharar da take addabar birnin Kano.