A iya fahimtar da na yi wa duniya, na fahimci mafi yawancin matsalolin da ke damunmu, mu muke jawo wa kanmu sanadiyyar rashin tsayawa inda Allah Ya tsayar da mu, kuma sai muke rika kokarin magance su ba tare da mun dawo kan wannan tafarkin da Allah Ya dora mu ba. Kuma lallai abu ne wanda har abada ba zai yiwu ba.
Allah (SWT) Ya yi wa kowace halitta ta duniyar ne halitta daidai da ita, ta yadda za ta ji dadin rayuwarta ta kuma kare kanta daga dukkan abin da zai cutar da ita, ba wai dan Adam ba kawai,
Misali, hawainiya da take tafiya sannu-sannu, ba kamar zomo ba ce da kan iya shekawa da gudu idan ya ga abin da zai cutar da shi, kuma ba irin mage da ke iya turjewa ta tayar da gashin jikinta don ta ba kanta kariya idan ta ga abu na neman wuce gona da iri ba, sai Allah Ya halicce ta (Hawainiyar) da wasu dabi’u guda biyu: Allah Ya halicce ta da dogon harshe, ba sai ta sauko daga kan itace ba take shan ruwan da ke kasa. Wannan kuma saboda kada idan ta sauko ta hadu da barazana tun da ba za ta iya gudu ba. Idan kuma larurar ta sauko kasa ta kama, to da ta tsinkayi wani abu da zai iya cutar da ita, nan take takan iya sauya launin jikinta ya dawo daidai da duk abin da ke kusa da ita, yadda ba za a ma fahimci akwai wata halitta a gurin ba.
Haka ma a wurin halittar dan Adam, da Allah Ya halicci jinsin maza da mata sai ya halittawa kowa yanayin jikinsa daidai irin yanayin aikin da ya fi dacewa da shi. Kuma tsarin da Allah Ya bayar shi ne namiji ya ciyar da mace, ya shayar da ita kuma ya tufatar da ita! Wannan ma shi ne fifikon da namiji yake da shi a kan mace kamar yadda Alkur’ani mai girma ya bayyana mana.
Allah Bai halicci mace da surar da za ta iya amfanar da kanta ba ballantana ta amfanar da wani ta wannan bangare. Matan da za ka ga ana yi musu kasuwanci da dukiyarsu za ka samu mazansu ne masu kudi ko kuma mahaifansu maza.
Matan an halicce su ne domin su natsar da mazajensu da Allah Ya halatta musu. A takaice dai abin da nake son in ce a nan, mace ba ta da wani aiki a duniya da ya wuce ta yi aure ta haihu, ta kula da mijinta da kuma tarbiyyantar da ‘ya’yanta bisa ga tsari na addinin musulunci! Duk wani abu da ba wannan ba, ko da kuwa abin kirki ne, to yana biyowa ne bayan ta tsayar da wannnan wajibin.
To amma wannan wajibin zai iya tabbatuwa ba tare da ilmi kyakkyawa ba? Ba zai yiwu ba! Amma wane ilmi? Tabbas ba wani ilmi da zai gyara tarbiyyar mace har ta tarbiyyantar da ‘ya’yanta face ilmin addinin musulunci. Boko zalla ba zai iya tarbiyyantar da ‘ya mace ba har abada. Babu mahaifin da zai iya bugun gaba ya ce ya kai ‘yarsa boko ne don ta samu kyakkyawar tarbiyya, ba gaskiya ba ne. Wayewar boko ce dai kawai take ba shi sha’awa ko kuma yana ganin ba ya son ya mutu ya bar ‘yarsa alhali ba ta iya daukar kanta! Don haka zai saka ta boko bisa fatan za ta samu sakamako mai kyawu da zai kai ta ga yin aikin gwamnati.
Iyayen da suke nufin ‘ya’yansu da samun tarbiyya mai kyau, sukan gabatar musu da ilmin addini ne kafin na boko. Ko kuma su hada musu guda biyu a waje daya (boko da na addini) Wadannan mahaifan ne za ka samu ba damuwarsu sai an kammala digiri a yi aure ba! Sai dai suna fatan su aurar da ‘ya’yansu a daidai lokacin da suka ga akwai bukatar hakan. Amma iyayen da ba tarbiyyar ce babban burinsu ba, za ka samu ba su damu da halayyar da tarbiyyar ‘ya’yansu take a ciki ba. Burinsu kawai ta yi boko kada ta wulakanta.
A karkashin wannan fahimtar ne wasu ke ganin cewa idan mace ba ta zare damtse ba ne ta yi boko dari bisa dari da zaran mijinta ya rasu ko ya sake ta za ta samu matsala! Wai za ta rasa madogara tun da ba ta da wata harkar yi (wanda hakan ke haifar da ba ilmin addini baya domin na boko ya samu gindin zama). Sun manta da cewa ba fatan ake yi idan miji ya rasu ko ya saki mace ta dawo gida ta zauna ba, kuma sun manta da cewa mazajen da su matan ke aure ne ba mazajen da ya dace a aura ba. Ai akwai namijin da Manzon Allah (SAW) ya ce a aura.
Idan ma hujjarsu a bar kamawa ce, shin matsalolin da matan ke cin karo da su na lalacewar tarbiyya da aikata fasikanci a fili (sanadiyar boko zalla) bai kai munin da ya kamata ta a tsaya a yi karatun ta natsu ba? Al’amari ya riga ya lalace, musamman a jami’o’i! Saboda haka akwai bukatar mahaifa su rika ba karatun addinin ’ya’yansu matukar muhimmanci kafin na bokon ma.
Nasir Abbas Babi 08033186727
Boko zalla ba zai iya tarbiyyantar da mace ba
A iya fahimtar da na yi wa duniya, na fahimci mafi yawancin matsalolin da ke damunmu, mu muke jawo wa kanmu sanadiyyar rashin tsayawa inda…