Mayaƙan Boko Haram sun kai hari ƙauyen Shikarkir da ke Ƙaramar Hukumar Chibok, a Jihar Borno, inda suka ƙone wata coci da gidaje.
Wannan hari na zuwa ne kwana ɗaya, bayan wani hari da suka kai ƙauyen Bazir, inda suka kashe mutum biyu sannan aka ƙone wata coci.
- DAGA LARABA: Dalilan ɓaraka a tsakanin iyayen riƙo da ’ya’yan riƙo
- Jami’ar Jihar Gombe ta rantsar da sabbin likitoci 56
A cikin wata sanarwa kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Nahum Daso, ya fitar, ya tabbatar da faruwar harin.
“Zaman lafiya ya dawo, kuma an ƙara tsaurarq tsaro. Muna tattara bayanai da kuma haɗa kai da sauran hukumomi domin tabbatar da tsaro da hana sake kai hare-hare.”
Wani mazaunin ƙauyen, Mallam Daniel Shikarkir, wanda gidansa ya ƙone, ya bayyana halin da ya shiga.
“Iyayena tsofaffi sun tsira ba tare da sun samu rauni ba, amma halin da muke ciki abun tsoro ne.
“Kwana ɗaya kafin wannan harin, maƙwabtanmu sun fuskanci irin wannan hare-hare, yanzu kuma ya zo kanmu.”
Shi ma, shugaban al’umma yanmin, Paul Mauntah Yaga, ya bayyana damuwarsa a shafinsa na sada zumunta, inda ya ce,
“Yanayin tsaro a Chibok yana ƙara tabarbarewa. Duk da kasancewar sojoji, hare-haren na ci gaba da faruwa.
“Muna roƙon shugabanninmu da su turo mana ƙarin jami’an tsaro domin kare al’ummominmu.”
A ƙauyen Dumba kuwa, har yanzu ba a gano gawarwakin manoma 40 da Boko Haram suka kashe a wani hari suka kai.
Wani da ya tsallake rijiya da baya ya ce, “Har yanzu ba a gano sauran gawarwakin waɗanda suka rasu ba.
“Har yanzu suna gonakin saboda ba za a iya zuwa wajen ba.”
Sojoji sun ce sun ceto mutum 271 daga cikin waɗanda suka tsira daga harin a Dumba.
Amma har yanzu ana ci gaba da damuwa kan yawan mutanen da suka rasa rayukansu.
Wani daga cikin mazauna yankin ya ce, “Mutanen da suka mutu sun haura 100, amma a gaskiyar lamari har yanzu ba a tantance su ba.”