✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta sako mata 48 da ta sace bayan karbar kudin fansa

Boko Haram ta sako mata 48 da ta sace daga kauyukan Maiwa da Shuwarin da ke Karamar Hukumar Mafa da ke Jihar Borno.

Kungiyar Boko Haram ta saki akalla mata 48 da ta sace a kwanakin baya a kauyukan Maiwa da Shuwarin da ke Karamar Hukumar Mafa da ke Jihar Borno.

An  sace matan ne a gonakinsu a ranar Talata 22 ga watan Agusta, kamar yadda wani mai bincike kan ayyukan ta’addanci a Yankin Tafkin Chadi, Zagazola makama ya bayyana.

Ya ce bayan da aka sace matan ne daga baya ’yan Boko Haram din suka bukaci iyalansu matan da su biya su kudin fansa.

A ranar 23 ga watan Agusta ne aka sako matan bayan an biya Naira 50,000 a matsayin kudin fansar kowannensu ga ’yan ta’addan.

An saki takwas daga cikin wadanda lamarin ya shafa tun farko bayan biyan Naira 20,000 kowannensu, in ji Zagazola.