✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta sake tarwatsa turakun raba wutar lantarki a Borno

Motar jami'an Sibil Difens da ke kai wa sojoji ɗauki ta taka bom a Borno

Mayakan Boko Haram sun kai farmaki a Jihar Borno inda suka yi amfani da bom suka tarwatsa manyan turakun rarraba wutar lantarki.

Wata majiyar soji da mazauna sun ce mayaƙan sun kai harin ne da misalin karfe 9 na dare a ƙauyen Garin Kuturu, daura da garin Auno a Karamar Hukumar Konduga.

Majiyar sojin ta ce, “Da muka ji karar abubuwan fashewan sai muka garzaya wajen, muka yi artabu da su, amma suka ki tserewa, saboda haka a sa mu a addu’a.

“Wani abin takaici shi ne motar  jami’an Sibil Difens da ke hanyar kawo mana ɗauki, ta taka bom din da ’yan Boko Haram din suka dasa.

“Ba zan iya cewa ko mutum nawa ne suka mutu ba, amma akwai wadanda suka rasu da wadanda suka ji rauni.”

Kakakin Runduna ta 7 ta Sojin Kasa ta Najeriya, Laftanar-Kanar Ajemusu Y Jingina, da wakilinmu ya tuntuba, ya ce, “Gaskiya ba ni da labarin harin.”

Kimanin mako guda ke nan da mayaƙan Boko Haram a yankin Kasaisa suka tarwatsa manyan turakun rarraba wutar lantarki mai karfin 330KVA daga Gombe zuwa  Damaturu.

Harin na wancan lokaci ya jefa manyan biranen jihohin Borno da  Yobe cikin duhu.

Daga bisani Gwamnatin Tarayya ta jona Maiduguri da tashar iskar gas, Damaturu kuma da layin wutar lantarkin Gombe zuwa Potiskum.