Mayakan Boko Haram sun kai farmaki a Jihar Borno inda suka yi amfani da bom suka tarwatsa manyan turakun rarraba wutar lantarki.
Wata majiyar soji da mazauna sun ce mayaƙan sun kai harin ne da misalin karfe 9 na dare a ƙauyen Garin Kuturu, daura da garin Auno a Karamar Hukumar Konduga.
Majiyar sojin ta ce, “Da muka ji karar abubuwan fashewan sai muka garzaya wajen, muka yi artabu da su, amma suka ki tserewa, saboda haka a sa mu a addu’a.
“Wani abin takaici shi ne motar jami’an Sibil Difens da ke hanyar kawo mana ɗauki, ta taka bom din da ’yan Boko Haram din suka dasa.
“Ba zan iya cewa ko mutum nawa ne suka mutu ba, amma akwai wadanda suka rasu da wadanda suka ji rauni.”
Kakakin Runduna ta 7 ta Sojin Kasa ta Najeriya, Laftanar-Kanar Ajemusu Y Jingina, da wakilinmu ya tuntuba, ya ce, “Gaskiya ba ni da labarin harin.”
Kimanin mako guda ke nan da mayaƙan Boko Haram a yankin Kasaisa suka tarwatsa manyan turakun rarraba wutar lantarki mai karfin 330KVA daga Gombe zuwa Damaturu.
Harin na wancan lokaci ya jefa manyan biranen jihohin Borno da Yobe cikin duhu.
Daga bisani Gwamnatin Tarayya ta jona Maiduguri da tashar iskar gas, Damaturu kuma da layin wutar lantarkin Gombe zuwa Potiskum.