✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta sace matafiya 9 a iyakar Najeriya da Nijar

An sace matafiyan ne a wani ƙauye da ke iyakar Najeriya da Nijar.

Wasu rahotanni sun bayyana cewar mayaƙan Boko Haram sun sace wasu matafiya a yankin Kumadouku da ke kan iyakar Najeriya da Nijar.

Masanin kan harkar tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagàzola Makama ne, ya bayyana hakan inda ya ce lamarin ya faru a ranar 22 ga watan Agusta, 2024.

Ta ce ’yan ta’addan su shida ɗauke da makamai, sun farmaki wasu motocin Najeriya da ke tsakanin kauyen Muria da Walada, a kusa kogin Kumadouku da ke kan iyakar Nijar, tare da yin awon gaba da fasinjoji tara.

A cewarsa, sun kai harin nd a kan dawakai, inda suka sace maza bakwai da mata biyu.

Wasu Daga cikin waɗanda aka sace sun haɗa da Kuriya Mallam Kura, daga Damasak Central, Yusufu Yau Ustass, daga Hausari Ward, Damasak, Ya’gana Malam Hassan, wata  mata, daga Damasak.

Ɗaya daga cikin ’yan uwan waɗanda aka sace, Yusufu Ya’u Ustaz, ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen suna neman a biya su kuɗin fansa Naira miliyan biyar.

Ya zuwa yanzu babu labarin inda mutane tara da motocin biyu suka shiga.