✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta kwace garin Marte

A ranar Lahadin da ta wuce ne jaridar Aminiya ta samu labarin yadda kungiyar Boko Haram ta samu nasarar mamaye garin Marte da ke Karamar Hukumar…

A ranar Lahadin da ta wuce ne jaridar Aminiya ta samu labarin yadda kungiyar Boko Haram ta samu nasarar mamaye garin Marte da ke Karamar Hukumar Marte da ke Jihar Bonro.  Garin Marte dai shi ne hedkwatar karamar hukumar Marte.

Kamar yadda rahoton ya nuna, ’yan kungiyar Boko Haram sun samu nasarar mamayar sojojin da ke Balatiya ta 153 da ke da alhakin kula da tsaro a yankin ne da misalin karfe 6 na yamma ana gab da shan ruwa inda suka rika yin harbin kan mai uwa da wabi, ba tare da kashe ko raunata wani ba da hakan ya nuna aniyarsu ta kwace garin don ya zauna a karkashin ikonsu.

Rahoton ya kara da cewa, wani mazaunin garin wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya shaidawa Aminiya cewa suna zaune da misalin karfe 6 na yamma sai suka ji tashin harbe-harben bindigogi al’amarin da ta sa kowa ya ranta a cikin na-kare.  Sai dai ya nuna babu wanda aka kashe ko raunata amma akwai tabbacin ’yan kungiyar ne suka kai hari garin na Marte inda suka karbe ikon garin daga jami’an tsaro.

Shi ma wani soja da ke aiki a karkashin Balaliyar wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya tabbatar da aukuwar lamarin.  “Da misalin karfe 6 na yammacin ranar Lahadin da ta wuce ne ’yan kungiyar Boko Haram suka mamaye mu suka kai mana hari.  Kodayake mun yi bata-kashi da su, amma saboda sun fi mu karfi da yawan makamai ya sa tilas muka gudu cikin daji don kada su gama da mu.  Kuma mun yi haka ne a matsayin wata dabarar yaki amma da zarar mun shirya za mu sake tunkararsu don sake kwato garin na Marte.

Ya zuwa hada wannan rahoto ba mu samu labarin korundunar sojin ta samu nasarar sake kwace garin na Marte daga kungiyar Boko Haram ba.

Matsalar tsaro dai tana kara tabarbarewa a fadin kasar nan al’amarin da ya sa da yawa daga cikin ’yan kasa suke yin kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya dauki matakin gaggawa don kawo karshen al’amarin musamman ta yi wa shugabannin hukumomin tsaro garambawul a wannan zangon mulkinsa na biyu.