✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta kashe jami’an tsaro 23 a Borno

Kungiyar ta yi musu kwanto a mahaifar Mai Ba Da Shawara Kan Tsaron Kasa

Sojojin Najeriya 19 tare da ’yan sa-kai sun bakunci lahira a wani kwanton bauna da mayakan Boko Haram suka yi musu a Gudumbali da ke kusa da Tafkin Chadi.

Wata majiyar soji ta tabbatar da mutuwar jami’an tsaron da kuma jikkata wasu mutum 10 a harin.

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya kara da cewa an kawo wadanda harin ya ritsa da su Maiduguri babban birnin Jihar Borno.

A nata bangaren kungiyar ISWAP ta yi ikirarin cewa mayakanta sun kashe jami’an tsaro 33 da jikkata wasu kusan 20, yayin da suka kama wani a matsayin firsinan yaki a Monguno, Jihar Borno.

Monguno ita ce mahaifar Mashawarshin Shugaban Kasar Najeriya kan Harkokin Tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno mai ritaya.

Kungiyar ta bayyana gawarwakin 15 da ta ke riya cewa na sojoji ne, da wasu motoci bakwai da makamai da ta ce mayakan nata sun kwace daga hannun sojojin.

Harin na ranar Asabar na daga cikin na baya bayan nan a rikicin Boko Haram da ya yi ajalin sama da mutum 36,000 da tilasta wa daruruwan dubban mutane gudun hijira a tsawon shekaru 12.