✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta mamaye sansanin sojoji ta sace makamai a Borno

Mayaƙan Boko Haram sun ƙwace sansanin sojin Najeriya inda suka kashe sojoji da ’yan sa-kai suka sace makamai a Jihar Borno

Mayaƙan Boko Haram sun kashe sojoji da ’yan sa-kai da dama wani sansanin sojoji da ke Ƙaramar Hukumar Damboa ta Jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun shaida mana cewa ’yan ta’addan sun yi awon gaba da makamai masu yawa bayan harin da suka kai da yammacin ranar Asabar.

Shaidu a majiyoyin tsaro sun bayyana saboda yawan ’yan ta’addan dole suka ƙwace sansanin sojin, amma jami’an tsaron sun ƙoƙarta.

Wani jami’in tsaro ya ce, “an sha kawo wa sansanin hari a baya amma wannan ne ya fi muni domin ’yan ta’adda sama da 100 suka kawo hari. Sun kashe sojoji da ’yan sa kai sun kwashe  duk makaman sun kona motoci da gine-gine.

“Da farko wani babban jirgi mara matuƙi suka turo, wanda muka ɗauka na sojoji ne da ke yin sintiri, kafin su far mana.

“Ba zan iya faɗin iya mutanen da aka kashe mana ba, amma dai mun gano gawarwaki 12. Mun samu labarin daga yankin Madara Gau da ke Ƙaramar Hukumar Biu suka kawo mana harin,” a sansanin da ke yankin Sabon Gari.

Jami’in tsaron ya ce a nan ne ƙungiyar ta ƙwace wata karowar gona inda ta mayar da ita sansani ga mayaƙanta.

Wata majiyar tsaro tabbatar cewa a baya-bayan nan mayakan Boko Haram suna yawan amfani da jirage marasa matuƙa wajen yin sintiri a yankin da ke tsakanin Chibok zuwa Biu.

Wani jami’in tsaro, Adamu, ya yi zargin cewa ’yan Boko Haram da ke tserewa daga yankin Tafkin Chadi ne ke hadu da sauran a yankin Da bisa suna hana zaune tsaye.

Ana iya tuna cewa dakarun sojin ƙasar Chadi sun tsananta bibiya da ragargazar Boko Haram tun bayan da kungiyar ta kashe sojojin kasar 40.