✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta ƙona wuraren ibada da gidaje a Adamawa

Mayaƙan Boko Haram sun kai hari a cikin dare inda suka ƙona wuraren ibada da gidaje da makarantu da shaguna a ƙauyen Kwapre da ke…

Mayaƙan Boko Haram sun kai hari a cikin dare inda suka ƙona wuraren ibada da gidaje da makarantu da shaguna a ƙauyen Kwapre da ke yankin Sabuwar Yadul a Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa.

Gabanin Sallar Isha’ a ranar Talata ne mayaƙan suka far wa yankin da hari, inda suka yi ta cin karensu babu babbaka.

Mazauna sun bayyana cewa maharan sun ƙona wuraren ibada da makarantu da gidaje da shaguna sannan suka sace dukiyoyin jama’a.

Mai unguwar kauyen Kwampre da Joel Kulaha, ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ce ba a samu asarar rai ba.

Ya bayyana cewa mazauna yankin sun tsare bayan farmaki da ’yan ta’addan suka kai musu.

“Mun samu tsira da rayukanmu, amma mu rasa duk wani abu da muka mallaka,” in ji shi, yana mai cewa babu dalilin harin da aka kawo musu.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin da aka girke a yankin Garaha da ke kusa da wurin sun kawowa al’ummar ɗauki, inda suka yi artabu tare da fatattakar maharan.

Sai dai mazauna na zargin cewar jami’an tsaron sun yi jinkirin zuwa, shi ya sa maharan suka yi ɓarna fiye da kima.

Wakilinmu ya yi ƙoƙarin zantawa da kakakin Birget na 23 na rundunar Sojan Najeriya, A. S. Adewunmi, amma jami’in bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da aka aika masa ba.