✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Boko Haram na shirin kai wa jirgin kasan Abuja-Kaduna hari —DSS

Barazanar harin na zuwa ne kasa da sati uku da dawowar sufurin jirgin kasan

Kasa da sati uku da dawowar jirgin kasan Abuja-Kaduna bayan harin 2022, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gano shirin kungiyar Boko Haram na sake kai masa hari a ’yan kwanakin nan.

Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya ce ta sanar da hakan a wata takarda da ta aike wa Ma’aikatar Tsaro, tana bukatar a dauki mataki.

Ma’aikatar ta ce DSS ta sanar da ita gane da yunkurin harin Boko Haram din ne tun a ranar 1 ga watan Fabrairu da muke ciki.

A kan haka ne ta jaddada bukatar Ma’aikatar Tsaron ta dauki gargadin da muhimmanci tare da kiran taron gaggawa na masu ruwa da tsaki domin shawo kan barazanar harin.

Sabuwar barazanar harin na zuwa ne kasa da wata guda bayan dawowar jirgin kasan na Abuja-Kaduna aiki tun bayan harin bom da ’yan bindiga suka kai masa, inda suka sace kimanin mutum 60 tare kashe wasu kimanin 10.

A jajibirin watan Ramadan na shekarar 2022 ne ’yan ta’adda suka kai wa jirgin kasan ta da ya baro Abuja da Magariba harin, ’yan kilomitoci kadan kafin ya sauka a Tasharsa da ke Rigas a Kaduna.

Sai da mutanen da maharan suka sace suka shafe wata takwas a hannun ’yan bindigar kafin su sako su, bayan an jima ana kai ruwa rana da kuma matsin lamba da gwamnati ta yi ta sha.

Harin na ranar 28 ga watan Maris ya jawo harkokin sufurin jirgin kasan, wanda galibi mutane kan shiga ne saboda guje rashin kayan hanyar Abuja-Kaduna da kuma matsalar ’yan ta’adda da ke garkuwa da mutane a kan hanyar.