✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram: Jami’an tsaro sun kwashe mutane daga Jakana zuwa Bakassi

A karshen makon jiya ne jami’an tsaro a Jihar Borno suka kwashe mutanen garin Jakana da ke Karamar Hukumar Konduga, mai nisan kilomita 40 daga Maiduguri,…

A karshen makon jiya ne jami’an tsaro a Jihar Borno suka kwashe mutanen garin Jakana da ke Karamar Hukumar Konduga, mai nisan kilomita 40 daga Maiduguri, zuwa sansanin gudun hijira na Bakasi da ke birnin Maiduguri.

Kwashewar ta biyo bayan tabbatar da rade-radin da jami’an tsaro suka dade suna ji cewa akwai wadansu daga cikin mutanen garin da ke taimaka wa Boko Haram da abinci da bayanai da wasu ababen more rayuwa, abin da kuma ake ganin zai iya  taimaka wa Boko Haram cin galaba a kan jami’an tsaro da su kansu al’ummar garin. Jami’an tsaron sun ce dole ne sun tantance mazauna garin kafin su ci gaba da zama, wanda hakan ya sanya aka tura manyan motoci sama da 30 don kwashe mutanen daga garin, abin da ya haifar da tsaiko wajen tantance mutanen kafin shiga sansanin gudun hijira na Bakasin.

Malam Ibrahim Garba,  daya daga cikin mutanen da aka kwaso daga garin Jakana zuwa Sansanin Bakasi ya ce, “Tun jiya da safe masu unguwanni da hakimai suka tara mu a kofar gidan Lawani suka ce kowa ya dauki Alkur’ani Mai girma, ya rantse cewa bai da  alaka da kungiyar Boko Haram ta fuskar taimaka musu ko bin akidarsu. To bayan kammala rantsuwar sai muka watse, kuma watsewarmu ke da wuya sai labari ya ishe mu cewa sojoji sun zo da manyan motoci za su kwashe mu zuwa Maiduguri mu da iyalanmu” Ya kara da cewa, “Haka muka shiga shirye-shiryen zuwa sansanin gudun hijira na Bakasi, amma jami’an tsaron ba su barI mun dauki wasu muhimman kayayyakinmu ba akasarinmu mun dauki tufafinmu ne kawai suka ce za mu je mu tarar da abinci a can, saboda wai suna gudun kada wani a cikinmu ya dauki wani abin fashewa irin su bama-bamai. Sun kawomu nan Bakasi an ki yarda mu shiga sun ce wai sai sun tantance mu kafin mu shiga, duk da wannan yawa da muke da shi. Ga zafin rana ga kananan yara da mata, ga shi ba mu da isasshen abinci, a takaice dai muna cikin mummunan yanayi a yanzu.’’

Malam Mamman Bukar, da shi ma ke cikin mutanen garin Jakanan da aka dawo da su sansanin Bakasi, ya ce, “Ni dan kasuwa ne a Jakana don ina da shaguna ina sayar da kayayyakin bukatun yau da kullum, kuma ina kiwon dabbobi, to amma abin bakin ciki an sanya ni dole na fito ba tare da shirin yadda zan tsare dukiyoyina ba, don an fito da mu ne cikin gaggawa ban kulle kofofin shagona ba kuma ban kammala bai wa dabbobina ruwa ba, kai a takaice ina cikin damuwa da tashin hankali.”

Ya ce  bai san halin da dukiyoyinsa suke ciki ba a yanzu, kuma ta fuskar iyali shi kadai aka sanya a mota suka taho, sai daga baya ya samu labarin cewar iyalinsa da yara za su zo daga baya.

Jami’an tsaro na sojin samar da zaman lafiya a karkashin Opration Lafiya Dole da Rundunar Soji ta Bakwai da ke garin Maiduguri da kuma Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (NEMA) suka fitar da sanarwa mai cewa,  “An kwashe mutanen Jakana ne zuwa sansanin na Bakasi a Maiduguri da nufin tserar da su daga harin Kungiyar Boko Haram da ake tsoron za su kai wa garin, tare da tantance su daga zargin alaka da kungiyar ta Boko Haram.