✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram: Ban da tubar muzuru

Hausawa kan ce “Kowa ya tuba don wuya ba Lada ba” … Idan har mutum zai dauki makami yana aikata ta’addanci ga wadanda ba su…

Hausawa kan ce “Kowa ya tuba don wuya ba Lada ba” … Idan har mutum zai dauki makami yana aikata ta’addanci ga wadanda ba su ji, ba su gani ba, ya yi fyade, ya yi kisa, ya yi garkuwa, ya kona mai rai, ya yanka, duk ba tare da tausayi ba. A neme ka sulhu don ka daina hakan a kuma yi ma afuwa.  A hada ka da ALLAH, wanda ka ce don shi kake yi, amma duk ka yi fatali da mutane kana takama da jiji da kai da alfahari da wannan sa6on, domin kana da bindiga kuma wasu tsinannu, la’anannu sun daure ma gindi.
Kodayake ban yi mamaki ba. Lokacin da naji cewa ‘Yan Boko-Haram sun fara kai kansu ga jami’an tsaro, domin tuni ruwa ya kare wa dan kada.  Domin “duk wanda ya ce ba ya tsoron wuta, ku nuna masa murhu.” A baya sun samu damar cin karensu har gashin sa, saboda rashin daukar matakan da suka dace a bangaren wadanda ke da alhakin daukar matakan.
Cikin kiftawa da bismila, sai ga shi yau sun fara cizon yatsa, dama ai karshen alewa kasa ne, kuma duk wanda bai ji bari ba, zai ji wowo. Don haka nake kira ga hukumomin Najeriya da shugabannin tsaron kasar, ka da su lamunci wannan rainin hankalin, tunda al’ummar Najeriya musamman na Arewa- maso-Gabas da rikicin nan ya durkusar da mu, ya nakasar da mu bayan ALLAH ya ba mu cikakkun halitta, ya tarwatsa mu, ya yi mana sanadiyar rabuwa da dimbin masoya; ya janyo mana tsangwama a ko ina, da sauran tarin abin da muka gani a dalilin wannan ta’addanci, wanda ba zai rubutu ba.
Muna kira da cewa “A dAUKI MATAKIN AZABTAR DA WAdANNAN AZZALUMAN, TSINANNUN. LA’ANANNUN, BABU SASSAUCI” Kamar yadda suka gasa mana aya a tsakiyar tafin hannu. Ba mu amince da duk wata nadama da suka yi ba.  Domin ai da-na-sani keya ce, kuma ba ta magani. Sannan ba adalcin da ya fi ga mutum “Yau ya girbi abin da ya shuka jiya.”  
Usman Bin-affan Damaturu: 08038001563