’Yan sanda a jihar Ogun sun cafke wani boka mai suna Samson Ogundele, bisa zargin yi wa wata mata fyade bayan ta je wajensa ba da shaida.
Wanda ake zargin, wanda mazaunin unguwar Refurefu ne da ke yankin Oja Odan a karamar hukuma Yewa ta Arewa, an kama shi ne bayan an kai karar shi ofishin ’yan sanda na yankin.
- An dawo da dokar hana hawa babur da daddare a Katsina
- Jirgin farko dauke da hatsi ya bar Ukraine zuwa kasuwar duniya
Kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa manema labarai a Abeokuta, babban birnin jihar ranar Lahadi cewa matar, wacce ke sana’ar kitso ta je wajen bokan ne saboda ya gano mata inda wasu kudinta Naira 100,000 da suka bace a shagonta suke.
Ya ce dukkan mutanen da suke shagon a lokacin sai da aka kai su wajen bokan a kokarin gano ainihin wanda ya dauki kudin.
Oyeyemi ya kuma ce, “Bayan an je gidan bokan, sai ya fara kiransu daki daya bayan daya, bayan ya karbi N700 daga hannunsu.
“Wacce take karar ta kuma shaida mana cewa mutum biyun farko da suka shiga sun fito, amma da lokacin shigarta ya zo, sai ya yi kokarin yi mata fyade.
“Hakan ce ta sa bayan karbar korafi DPO na yankin, CSP Gabriel Ikechukwu, ya umarci dakarunsa da su gaggauta kamo shi.
“Ana cikin tuhumarsa ne sai daya daga cikin ’yan matan da ya gana da su, mai kimanin shekara 17 ta tabbatar da cewa ya riga ma ya yi mata fyade lokacin da suka kebe a daki.
“ta kuma ce ya yi mata barazanar cewa muddin ta kuskura ta fada wa wani, za ta mutu.
“Daga nan ne muka garzaya da ita Babban Asibitin Oja Odan, inda likitan da ke aiki ya tabbatar da cewa an yi lalata da ita.”
Kakakin ya ce tuni bokan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.
Ya kuma ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Lanre Bankole, ya ba da umarnin mayar da wanda ake tuhumar Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar domin fadada bincike.