Kamfanin X wanda aka fi sani da Twitter zai cire tsarin toshe sakonni da ke ba masu amfani da dandalinsa na sada zumunta damar toshe shafukan da ba sa son mu’amala da su.
Mai kamfanin, Elon Musk ya ce hakan zai cire wa masu amfani da X ƙaidin da ke takaita shafukan da za su iya tuntuɓar su, ganin saƙonsu ko bin su.
- Mali da Burkina Faso sun ba Nijar jirage don yaƙar sojojin ECOWAS
- Matsin rayuwa ya sa Magidanci rataye kansa a Jigawa
“X zai a cire damar toshe asusu amma ban da DMs,” in ji Musk a sakon da ya wallafa a kan dandalin a ranar Juma’a. Amma ya ce za a bar damar kayyade ganin sanarwar shigowar sakonnin asusun da mutum ya zaba wa kansa.
Sai dai sanarwar ta haifar da damuwa game da amincin masu amfani da X da kuma kayyade abubuwan da za a iya yi da shi.
Masu bincike sun gano karuwar kalaman kyama a dandalin tun lokacin da Musk ya zama shugaban kamfanin X bara, kuma wasu gwamnatocin sun zargi kamfanin da rashin yin abin da ya dace don daidaita abubuwan da ke cikinsa.
Sai dai Musk ya bayyana kansa a matsayin mai rajin kare ’yancin fadin albarkacin bakin, amma wasu masu suka sun ce matakin da ya dauka bai dace ba.