Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), ta ƙara sanya wa ’yan Najeriya da ke son ziyartar Dubai sabbin sharuɗa.
Haka kuma, ta dakatar da bayar da bizar wucin gadi ga ’yan Najeriya.
- Yara miliyan 5.4 na fama da karancin abinci a jihohin arewa 9 – Red Cross
- Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista
Aminiya ta samu labarin cewa hukumomin shige da fice na Dubai ne suka bayar da umarnin sabbin matakan ga ofishin jakadancin ƙasar da ke Najeriya.
Daga cikin sabbin dokokin, duk ɗan Najeriyar da ke tsakanin shekaru 18 zuwa 45 ba zai samu bizar yawon buɗe ido ba sai idan zai yi tafiya tare da wani.
Wannan na nufin cewa yawan ’yan Najeriya da ke tafiya Dubai zai ragu, duba da yadda birnin ke da farin jini wajen kasuwanci da yawon buɗe ido.
A bara UAE, ta janye haramcin biza da ta sanya wa ’yan Najeriya na tsawon shekaru biyu.
Amma janye haramcin ya zo ne da sharuɗa masu tsauri, kuma yanzu ta ƙara tsaurara su.
Wani muhimmin canji a cikin sabbin ƙa’idojin shi ne cewa ba za a ƙara neman bizar wucewa ba daga ’yan Najeriya.
Sannan duk wanda ya haura shekaru 45, sai ya gabatar da bayanin asusun bankinsa na tsawon watanni shida da suka gabata.
Kuma kowane wata dole ne asusun ya zamana akwai aƙalla dala 10,000 ko dai daidai da hakan a kuɗin Naira.
Ƙasar ta ce dole ne a cika waɗannan sharuɗan tare da sauran takardun da ake buƙata da bayanan fasfo.