✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bishop Kaigama ya bukaci al’umma su yi zabe cikin lumana

Bishop cin Cocin Katolika na Jos kuma Shugaban Bishop-Bishop din Katolika na Nijeriya, Akbishop Ignitius Kaigama ya roki al’ummar Najeriya su yi zaben da ake…

Bishop cin Cocin Katolika na Jos kuma Shugaban Bishop-Bishop din Katolika na Nijeriya, Akbishop Ignitius Kaigama ya roki al’ummar Najeriya su yi zaben da ake shirye-shiryen gudanarwa a watan gobe cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Akbishop Kaigama ya yi wannan roko ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a Jos, inda ya ce “Muna rokon a yi komai cikin kwanciyar hankali a lokacin wadannan zabubbuka da za a gudanar kuma a bai wa wanda al’umma suka zaba.”

Har ila yau ya yi kira ga hukumomin da aka ba su ikon gudanar da zabubbukan su yi bisa tsoron Allah. Kada su yi kokarin cutar da wani mai zabe ko wani dan takara. Ya ce hukumomin tsaro su ji tsoron Allah kada su musguna wa mutane a lokacin zabubbukan. Kuma kada a tsoratar da mutane ko a hana mutane zaben wadanda suke so.

Sannan ya yi  kira ga ’yan siyasa su guji tura magoya bayansu suna far wa juna, suna kashe-kashe da lalata dukiyoyin jama’a kuma su taimaka wa al’ummar Najeriya a zauna lafiya.

“Ga talakawa da marayu da matan da mazansu suka mutu da matasa marasa aikin yi da yawa a Najeriya. Don haka ya kamata ’yan siyasar kasar nan su dubi wannan hali da al’umma suke ciki su tallafa masu,” inji shi.