✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Birtaniya ta horar da matan Najeriya 16,000 kan fasahar zamani

Akalla mata da ’yan mata 16,000 ne suka samu tallafin kasar Birtaniya a Najeriya albarkacin shirin hadin gwiwar Birtaniya da Najeriya a fannin fasahar zamani.…

Akalla mata da ’yan mata 16,000 ne suka samu tallafin kasar Birtaniya a Najeriya albarkacin shirin hadin gwiwar Birtaniya da Najeriya a fannin fasahar zamani.

Mataimakin Jakadan Birtaniya a Legas, Ben Llewellyn-Jones wanda ya samu wakilcin Kris Camponi, shi ne ya bayyana haka ranar Laraba a wajen taron horaswa da suka shirya wa ’yan mata a Legas.

Taron wanda aka shirya don bikin Ranar ’Ya Mace ta Duniya ta 2022, ya maida hankali ne kan tattauna muhimmancin ilimin fasaha ga rayuwar ’ya’ya mata.

Jami’in ya ce shirin ba da ilimin fasahar zamani na DAP, ya koya wa mata da ’yan mata sama da 16,000 ilimin fasaha a Najeriya wanda za su iya samun aiki da shi.

Haka nan, ya ce shirin DAP ya tallafa wa tattalin arzikin zamani na Najeriya ta hanyar gudanar da harkokinsa a kasar.

Llewellyn-Jones ya ce, Birtaniya kasa ce da ke kan gaba game da sha’anin ilimi, kuma tana da yakini ilimi na da matukar muhimmanci ga cigaban duniya.

Ya ce, bai wa ’ya’ya mata ilimi ya zama wajibi musmaman a Afirka saboda an baro su baya alhali su suka fi yawan al’umma.