✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Binciken Magu: Abin da Salami ya gaya wa Buhari

Buhari ya ce babu shafaffe da mai a batun yaki da cin hanci da rashawa

Kwamitin Shugaban Kasa mai binciken zargin dakataccen Shugaban Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci, Ibrahim Magu ya bukaci a rika ba da shugabancin hukumar ga jami’ai sauran hukumomin tsaro.

Shugaban Kwamitin Mai Shari’a Ayo Salami mai murabus ya bukaci Shugaba Buhari ya duba sauya wa jami’an ’yan sanda da ke EFCC wurin aiki.

Yayin mika wa Buhari rahoton binciken sa a ranar Juma’a, Mai Shari’a Salami ya ce ’yan sanda ne shugabannin EFCC tun da aka kafa ta.

“Tun daga aka kafa EFCC ’yan sanda ke jagorantar ta don haka ya kamata a idan za nada sabo a ba da dama ga mutanen da suka cancnata daga sauran hukumomin tsaro da EFCC kamar yadda dokar hukumar ta 2004 ta tanadar.

“Yanzu haka ’yan sanda 970 ne ke aiki a EFCC don haka a duba yiwuwar sauya su cikin shekara biyu masu zuwa domin magance matsalar rashin karin girman ainihin ma’aikatan hukumar na sama da shekara tara.

“Muna ba da shawarar duk wanda za a nada, matukar ba ainahin ma’aikacin EFCC ba ne, to ya kasance na rikon shekara biyu kafin a nada cikakken ma’aikacin hukumar da ya samu yabo daga hukumomin duniya saboda kwarewa a yaki da manyan laifuka”, inji Salami.

Ya ce Magu da shaidu 113 ne suka bayyana gaban kwamitin wanda ya karbi takardun korafi 46 a kan EFCC da tsohon shugabanta nata.

Ya ce Kwamitin ya zaga sassan Najeriya don tantance kadarorin gwamnatin da aka kwato na gidaje, motoci, jiragen ruwa da sauransu.

A cewarsa umarnin Buhari na sayar da kadarorin da aka kwato ya dace “duba da mummunan halin da muka gan su a ciki a lokacin zagayen”.