Babu shakka, Zamfara ce jihar da matsalar rashin tsaro da ayyukan ’yan bindiga, garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kuma satar shanu suka fi addaba a fadin Najeriya.
A wani yanayi mai cike da hatsari, sashen binciken kwakwaf na BBC Africa Eye ya yi dogon bincike, sannan ya fitar da wani rahoto a kan hakikanin musabbabin rikicin.
- Sabon fada ya barke tsakanin Hausawa da Yarabawa a Ibadan
- NAJERIYA A YAU: Muhammad Abacha Ya Ga Samu Ya Ga Rashi A Zaben PDP A Kano
Rahoton, wanda na bidiyo ne, ya gano cewa ana yin rikicin ne a tsakanin ’yan bindiga, wadanda galibinsu Fulani ne, da kuma ’yan sa-kai, wadanda galibinsu Hausawa ne.
Rahoton na tsawon minti 50, wani dalibi ne mai nazari a kan Harkokin Shari’a mai suna Yusuf Anka ya tattaro bayanan da aka hada shi da su; ya kuma gano cewa a yanzu rikicin ya koma daukar salon kabilanci tsakanin Hausawa [manoma] da Fulani [makiyaya].
Gundarin abin da ya kunsa
A Jihar Zamfara, wacce ke Arewa maso Yammacin Najeriya, kusan babu wanda ya tsira daga harin ’yan bindiga.
Wadannan maharan na kai hare-hare a kan babura dauke da muggan makamai kamar su bindiga kirar AK-47, sannan su kashe, su kona kadarori, su sace mutane, sannan su yi wa mata fyade.
Sukan bayyana a kan tituna ba zato ba tsammani, su harbe wasu fasinjoji su kuma sace wasu, sannan su yi cikin daji da wasu don neman kudin fansa.
Hatta kananan yara ba su tsira ba; an sace daruruwan yara a makarantun kwana da ke jihar an yi cikin daji da su.
A 2022 kawai, sama da mutum 35,000 ne aka kashe a fadin Najeriya, kusan miliyan daya kuma sun rasa muhallansu.
Sai dai galibi ba a jin rahoton wannan rikicin, saboda zuwa nemo labarinsa na da matukar hatsari ga ’yan jaridar da ke aiki a can.
Akwai dimbin tambayoyin da ’yan Najeriya suke ta yi a kan hakikanin abin da ’yan bindigar nan ke bukata.
Me suke so? Me ya sa rikicin ya ki ci, ya ki cinyewa?
A tsawon sama da shekara uku, shirin na BBC Africa Eye, ya yi kokarin kurdawa har maboyar jiga-jigan ’yan bindigar a jihar ta Zamfara don gano bakin zaren.
A cikin wani yanayi mai cike da hatsari, Yusuf Anka ya yi tattaki har cikin dazuzzukan da wadannan ’yan bindigar suke a fadin jihar, ciki har da wanda a watan Fabrairun 2021, ya jagoranci sace dalibai ’yan mata kusan 300 a Makarantar Sakandaren ‘Yanmata ta Jangebe da ke Jihar.
Kafin wannan lokacin dai, ba kasafai ake jin muryoyin wadannan ’yan bindigar a kafafen yada labarai ba.
Abin da rahoton ya gano
A cikin jerin tattaunawa daban-daban, rahoton ya gano tushen rikicin wanda ya tasam ma kassara jihar baki daya.
Ya kuma ce Najeriya, a matsayin kasa, ta gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummarta.
Rahoton ya gano yadda satar mutane domin karbar kudin fansa ta zama wani kasuwanci mai gwaggwabar riba, tare da yin gargadin cewa rikicin ya dauki wani salo na kabilanci.
Galibin wadanda suka yi magana a ciki dai sun hakkake cewa babu wani abin a-zo-a-gani da gwamnati ke kokarin yi wajen magance matsalar.
Su wane ne suke rikici da juna?
Rahoton ya kuma gano cewa rikicin ya fara ne a matsayin takaddama a kan filayen noma da kiwo da ruwan sha, kafin daga bisani sauyin yanayi da rashawa da talauci su kara ta’azzara shi.
Hausawa da Fulani sun yi daruruwan shekaru suna rayuwa tare da juna a Arewacin Najeriya. Sai dai bisa ga dukkan alamu, rikicin ’yan bindiga ya tasam ma kawo karshen wannan alakar.
Rahoton ya kuma cewa akwai batutuwa da dama da mutane ba su fahimta ba game da wannan rikicin saboda karancin rahotanni a kai.
Ya kuma yi duba na tsanaki a kan wadannan ’yan ta’addan da kuma bukatunsu da suka saka suka dauki makamai.
Ya kuma tattauna da rikakkun ’yan bindiga, ciki har da irinsu Ado Aleiro, wanda a kwanaki nadin sarautar da Masarautar ’Yandoton Daji ta yi masa ya tayar da kura, da irinsu Hassan Dantawaye, wanda ya jagoranci sace ’yan makarantar Jangebe, da dai sauransu.
A shekarar 2021 dai, rahotanni sun nuna cewa Zamfara ce jihar da ta fi kowacce yawan mutanen da aka kashe a duk fadin Najeriya.
Sai dai duk yunkurin da masu rahoton suka yi na jin ta bakin dakarun Najeriya don su yi tsokaci kan wasu zarge-zargen su da aka yi a cikin raohoton, ya ci tura, saboda sun ki su ce uffan a kai.
Dalilin jin ta bakin ’yan bindiga
Da yake zantawa da Aminiya a kan dalilin da ya sa BBC ta yanke shawarar zuwa har dazuzzukan da ’yan bindigar suka yi kaka-gida domin jin ta bakinsu, Yusuf Anka ya ce manufarsu ita ce fayyace musabbabin rikicin saboda mutane su fahimce shi
“Burinmu ba shi ne mu ba wani bangare bakin magana ba, sai dai don mu wayar da kan mutane su fahimci rikicin tun daga tushe.
“Mun yi aikin ne da zuciya daya ba tare da nufin goyon bayan kowanne bangare ba, kuma ba ma goyon bayan kowa.
“Ra’ayinmu kawai shi ne wanda bayanan bincikenmu suka nuna, ta hanyar jin ta bakin masu aikata barnar da wadanda aka aikata ta a kansu.
“Akwai mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, daga dukkan bangarorin rikicin guda biyu,” inji shi.
‘Sojoji sun taba kai hari ta sama ina cikin wani kauye’
Da muka tambaye shi yadda zai bayyana irin hatsarin da ya shiga a kokarin tattara rahoton, Yusuf ya ce akwai abubuwan da ba zai taba mantawa da su ba.
“Akwai matukar hatsari. Kowa ya san hatta tafiya a kan manyan titunan Zamfara a ’yan kwanakin nan yana da matukar hatsari, ballantana a yi maganar shiga dazuzzuka.
“Mun ziyarci kasurguman ’yan bindiga da dama.
“Akwai ma abin da ba zan taba mantawa da shi ba: wata rana na je daya daga cikin wadannan kauyukan sai jin ruwan harsasai muka yi sojoji sun kawo hari ta sama.
“A lokacin Allah ne kawai ya kubutar da ni, da tuni an kashe har da ni.
“Babban burinmu na yin wannan binciken kwakwaf din shi ne saboda gwamnatin Najeriya da ma sauran jama’a su fahimci rikicin da irin sabon salon da yake dauka a kullum.
“Mun kuma gano babu wani yunkuri da gwamnati take yi na kula da mutanen da rikicin ya shafa,” inji Yusuf Anka.
A baya-bayan nan dai an fara samun ”yan jarida suna shiga dazuzzukan da ”yan bindiga suke hira da su.
Ko a kwanan baya ma daya daga cikin editocin jaridar Daiy Trust ya ziyarci yankin, ina ya yi hira da wasu daga cikin jagororin ‘ya bindigar.