Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce binciken da majalisar jihar ta ba da shawarar a yi kan gwamnatinsa “bi-ta-da-ƙulli ne kawai na siyasa.”
Cikin wata sanarwa ta martani da Muyiwa Adekeye ya fitar a madadinsa, El-Rufai ya ce ya bauta wa Kaduna “da gaskiya kuma yana alfahari da abubuwan da ya yi.”
- Fiye da Naira biliyan 400 sun zirare a Gwamnatin El-Rufai — Majalisar Kaduna
- Mutum 62 sun mutu a harin da Isra’ila ta kai tsakiyar Gaza
“Muna tabbatar da gaskiyar gwamnatin El-Rufai tare da yin watsi da waɗannan iƙirari da ake yaɗawa,” in ji sanarwar.
“Ya [El-Rufai] bi duk wasu dokoki a ayyukansa lokacin da yake gwamna…ya kamata a yi watsi da wannan binciken na ƙeta a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa.”
A wannan Larabar ce Kakakin Majalisar Dokokin Kaduna Yusuf Liman ya yi zargin cewa kuɗin da suka kai naira biliyan 423 ne suka zirare a gwamnatin ta El-Rufai da kuma barin jihar da basuka.
Wani kwamiti da majalisar ta kafa ya ba da shawarar a binciki tsohon gwamnan da kuma wasu muƙarrabansa, ciki har da Kwamishinan Kuɗi, Akanta-Janar da sauransu.
Majalisar na wannan zargi yayin da ta buƙaci hukumomin da ke yaƙi da rashawa su binciki tsohon gwamnan da wasu muƙarraban gwamnatinsa kan zargin cin amanar aiki da halasta kuɗin haram.
Wannan na zuwa ne bayan bincike na musamman da wani kwamitin majalisar ya gudanar ƙarƙashin jagorancin Henry Magaji Danjuma.
A cewar rahoton da Henry ya gabatar a ranar Laraba, yawancin bashin kuɗin da aka samu a ƙarƙashin gwamnatin El-Rufai, ba a yi amfani da su yadda suka dace ba, kuma a wasu lokuta, ba a bi ka’idojin da suka dace wajen samun bashin ba.