A yayin da ake tsaka da gudanar da shagulgulan sallah, an samu akalla mutum 10 da suka rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin mota da ya afku a yankin Iyemoja a Jihar Kwara.
Bayanai sun ce mummunan tsautsayin ya auku ne a kan babbar hanyar Ilorin zuwa Jebba da ke Karamar Hukumar Moro.
- Gwamna Bala ne mafi dacewar Najeriya a 2023 —Matasan Arewa
- Hotunan yadda aka yi Babbar Sallah a Najeriya
Hatsarin ya rutsa ne da wata motar haya kirar Hiace mai daukar fasinja 19 da lambarta LND742XK da misalin karfe 3 na yammacin ranar Talata.
Sai dai ana zargin cewar gudun wuce kima ne ya haddasa hatsarin kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Wanda lamarin ya faru a kan idonsa ya bayyana cewar motar ta yi taho-mu-gama da wata mota.
Kazalika, mutum takwas sun ji rauni a sanadin hatsarin, wanda da dama daga cikinsu sun samu raunuka da suka hada da karaya.
Wakilinmu ya ruwaito cewa tuni aka garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa Asibitin Ayo, Okolowo da kuma Babban Asibitin Jihar inda aka basu kulawa cikin gaggawa.
An kuma killace gawawwakin mutum 10 da suka rasa rayukansu a dakin ajiye gawa na babban Asibitin Ilorin.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura (FRSC) na jihar, Jonathan Owoade ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ja hankalin masu tuka ababen hawa da su rika kula da yanayin tukinsu.
Har wa yau, ya jinjina wa jami’an ‘yan sanda na ofishin Oloje kan yadda suka kai dauki wajen da hadarin ya faru a kan lokaci.
Wannan hatsarin na zuwa ne kasa da mako guda, da wasu mutum 10 suka mutu, yayin da wasu tara suka ji rauni a hatsarin mota da ya faru a yankin Kanmbi na Karamar Hukumar Moro a jihar.