Da yawa daga cikin bukukuwan da Hausawa ke gudanarwa shekara-shekara, sukan yi su ne a cikin yanayi na musamman da zai dace don cimma nasarar aiwatar da su a tsanake. Saboda haka ne za a ga cewa yawancin bukukuwa masu ɗaukar kwanaki ana yin su ne da kaka. Haka a daidai wannan lokaci ne Hausawa suka fi samun sukunin gabatar da bukukuwan. Dalili shi ne saboda an girbe abin da aka shuka na albarkatun gona. wato kuɗi sun samu.
Bikin Kalankuwa biki ne na al’adar Hausawa, wato ba ya da wani tasiri da addinin Musulunci. Ana gudanar da shi ne shekara-shekara da kaka bayan an kawar da amfanin gona. Wasa ne mai kayatarwa da nishaɗantarwa da kuma motsa jiki. Yawanci samari da ’yan mata ne sukan shirya shi. Kuma yakan samu karɓuwa a duk inda ake gudanar da shi, jama’a kan taru daga wurare daban-daban domin irin wasannin da bikin ya ƙunsa. Ta haka ne ma ake kyautata zaton ya samo sunansa ne daga “Kallon kowa.”
Da zarar damina ta fadi maza kan roƙi iyayensu su ba su. “gayauna” daga cikin gonarsu domin su noma abin da za su sayar da kaka su samu kuɗin shirin wannan biki. ’Yan mata kuma kan yi kiwon dabbobi su sayar su ma domin shirin wannan biki, ko da yarinya ba ta yi wani ɗinki kamar na Sallah ba, za ka ga ta matsa wa kanta dole sai ta yi na bikin Kalankuwa. ’Yan mata kuma sukan yi tanadin abubuwa na musamman da za su yi wa samarinsu domin nuna bajinta da ƙauna da soyayya da sauransu.
A wannan biki ne ’yan mata ke bayar da ‘Badago’ ga samarinsu, su ma samarin su mayar da shi bayan kwana ɗaya. Yawanci akan zaɓi Sarkin Samari da Shugabar ’Yan mata su huɗu tare da sauran abokai da ƙawaye domin yin shawarwari a kan lokaci da mawaƙa da ire-iren ’yan wasan da za a gayyata domin gudanar da bikin. Yawancin shugaban biki wato Sarkin Samari da shugabar mata ke raba goron gayyata ga mawaƙa da maroƙa da ’yan wasan da za a gayyata na nesa da kusa bayan an tsayar da ranar da za a yi bikin, haka kuma a kasuwanni da ƙauyuka na kusa a matsayin gayyata. Haka samari da ’yan mata kan aika wa abokai da ƙawayensu na musamman irin wannan goron gayyatar, kuma su sukan zamanto masu masaukin baƙinsu.
Idan lokacin ya matso ne ake gyara wurin sauƙar baƙi da filin gudanar da bikin. Kamar yadda yake waɗanda aka gayyata sun haɗa da ’yan kokawa da ’yan dambe da makaɗan duma da wasan dabo da ’yan tauri da masu kiɗan kalangun ’yan mata da sauran manyan baƙi.
Yadda ake gudanar da bikin
An fi gudanar da wannan biki daga ranar Juma’a zuwa Lahadi a akasarin wuraren da ake yin sa. Wannan zai ba kowa damar zuwa. Baƙi da masu wasanni na hallara ne tun ranar Alhamis da yamma domin safiya na yi ranar Juma’a bikin ke farawa. Samari da ’yan mata na karɓar baƙinsu da shirya musu abinci. Ana hidimomin abinci iri-iri wani lokaci Shugabar mata kan dauki haya don yin abincin baƙi kawai. A wannan ranar ce ’yan mata ke ba samarinsu ‘Badago’ da yamma. Wani abinci ne na musamman da budurwa ke shirya wa saurayinta don nuna cewa shi take so. Yawanci takan haɗa da kaji da goro da sauran kayan lashe-lashe da tande-tanɗe da tsotse-tsote.
Bayan masu yin wasanni da safe sun gama da yammar wannan Juma’ar ’yan mata kan yi “Galma wuta.” A nan za ka ga ’yan mata fiye da ɗari sun ci ado, sun taru wuri ɗaya tare da maroƙa. Kowace za ta ɗauki abincin da ta shirya wa saurayinta a kanta ana tafe da makaɗa da maroƙa suna zagaya gari tare da kirare-kirare daga maroƙan baka. ’Yan mata na rera waka da amshi. Bayan sun zagaye gari kaf sai a taro dukkan abincin nan wuri ɗaya a dandalin wasa. ’Yan mata na komawa gida sai su sake cin wani adon da dare a fito wani taron, da kowa ya hallara sai makaɗan kalangu su barke da kiɗa.
A nan ne kowace budurwa za ta yi shirin ba saurayinta ‘Badago’. Su kuma samari dama duk sun zo wurin wasa tare da baƙin abokansu, kowa zai zura ido ya ga ko shi budurwarsa za ta ba Badago ko wani. Yawancin ’yan mata kan yi musayar Badago ne wajen raba shi. kowace ta faɗa wa ƙawarta saurayin da za ta ba abincinta. Saboda haka wannan za ta ɗauki na waccan.
A nan filin za a nufi saurayi da abinci daga budurwarsa, zai yi murna da kuri ga sauran samari musamman abokan takararsa a wajen yarinyar. Duk saurayin da aka ba Badago zai raba shi nan take ga abokansa kuma za su ba shi ’yar gudunmawa gwargwadon hali shi kuma zai aje kwanukan wurinsa kafin ranar mayarwa ta zo. Daga nan sai a goce da kiɗan kalangu ’yan mata na rawa samari na kashe kuɗi, wani na yin tambaya wani kuma na yin kari haka za a yi ta kashe kuɗi ana gasa har sai an ga wanda za a ƙure. Haka za a ci gaba da wannan gasar har sai kiɗa ya tashi.
A rana ta biyu. wato ranar Asabar nan ma wasanni za su ci gaba. Da hantsi fili zai cika. Da zarar fili ya cika sai a ba ’yan kokawa fili su fara. Makaɗa na ta kaɗa Gunduwa, wasu manyan ganguna ne masu ƙarar gaske. Ana kaɗa wa ’yan kokawa takensu suna fitowa suna tsima suna ihu da kirari, suna tarar juna ana gwabzawa ana liƙa kuɗi. Wata sa’a kuma ana sa “Kazar ƙarfi” ga ’yan kokawar. Ba a cika barin ’yan gari ɗaya su kara ba, sai dai tsakanin na wannan gari da wancan. Wata sa’a kuma ana iya tambaya ga mai karfin gaske da ake kira ‘Ƙaura,’ yawancin duk wanda aka naɗa Ƙaura ya gama yin kokawa sai dai ya zo kallo.
Sauran wasanni da akan gabatar sun haɗa da na Gangi, na manoma, da na bishi (kiɗan mafarauta) da wasan ’yan gambara da wasan shanci wato na ’yan dabo da sauransu. Bayan wasannin yamma idan an koma gida kowa ya ci abinci an huta. sai kuma a ɗunguma zuwa wurin kiɗan kalangu na ’yan mata da dare. A nan ne kuma samari aiki ya koma kansu.
A daren ne samari za su mayar wa ’yan mata kwanuknsu da aka kawo Badago. Saurayi kan sha wahala a wannan rana domin ba ya kai wa budurwa kwanukan haka nan, dole sai ya gwada irin tasa bajintar domin kuwa sai ya sayi kwalla ya zuba atamfofi da sarƙoƙi da ’yan kunne da takalma da man shafawa da hoda da su turare da kayan tsotse-tsotse har da su goro. Wadansu ma har da su rediyo. Idan saurayi ya kammala saye-saye yana tafiya da su cikin kwalla zuwa wurin kiɗa. Da ma ’yan mata duk suna zaune kan kujeru a cikin fili sun ci ado, idan saurayi ya sa tambaya, yakan ba maroƙi wasu ’yan kuɗi mai kiɗa kuma a ba shi masu ɗan yawa. Sannan ya ce a ba budurwarsa waɗannan kayan da wasu ’yan kuɗaɗe. A nan ne ake cewa saurayi ya mayar da Badago. A irin wannan wuri ne ake yin ɗaurin ’yan mata kowace budurwa ba ta da ikon ta tashi sai saurayinta ya kwance ta, a nan ma akan yi gasar har sai an ƙure wani. A cikin ’yan mata kuwa duk wadda ta rasa wanda zai kwance ta akan yi mata ba’a da waƙe-waƙen rashin jin daɗi har kiɗa ya tashi. A ranar Lahadi ma wasanni kan ci gaba kamar sauran ranaku ammna daga nan ne bikin Kalankuwa ke zuwa ƙarshe.
Al’ada da daɗi gun masu ita.