✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bikin Hawa dokin kara a Fagge

Duk yayin da aka yi bikin Sallah (babba ko karama), duk ranar Hawan Nassarawa; hawan da mai martaba Sarkin Kano ke zagayen unguwannin Nassarawa da…

Duk yayin da aka yi bikin Sallah (babba ko karama), duk ranar Hawan Nassarawa; hawan da mai martaba Sarkin Kano ke zagayen unguwannin Nassarawa da Fagge da wasu unguwannin don gaisuwa ga al’ummarsa na wadannan yankuna kafin ya isa gida, matasa da dattawa maza da mata na Unguwar Fagge kan yi dandazo domin tarbar mai martaba da gaisuwa gare shi. A ranar ce ake karfafa sada zumunci ga sarki da jama’arsa, sannan ga ’yan uwa da abokai da dangi da suke unguwar Fagge. A wannan ranar za ka ga kowa fes-fes cikin farin ciki da jin dadi.

Tun lokacin da mai martaba marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya fara rashin lafiya aka gutsire wannan hawa na Nassarawa, ya kasance sarkin ba ya biyowa ta cikin tsakiyar Unguwar Fagge, sai dai ya yi yanke, har zuwa yanzu da abin ya ci gaba. Haka shi ma mai martaba Sarkin Kano na yanzu, Muhammadu Sanusi II ya ci gaba da yin koyi da marigayi sarki, ta hanyar bi ta can titin Kantin Kwari, titin Plaza.

Wannan ta sa matasa maza da mata suka dauki al’adun yin hawa irin na Dokin Kara, domin kar a raunana wannan al’ada ta zumunta a tsakanin dimbin al’ummar da ke unguwar da kuma kasancewa cikin farin ciki da annashuwa. Yin wannan al’ada ta matasa ta maye gurbin da yawa daga gibin da aka bari na gutsire Hawan Nassarawar da mai martaba yake yi kuma ya dawo da abin da ake yi na sadar da zumunta ga juna da farin ciki ga juna.

Tabbas, wannan al’ada ta hawan dokin kara ga matasan Unguwar Fagge tana sanya dimbin al’umma farin ciki kuma tana sadar da zumunci. Al’adar tana sanya matasan tunanin yin kyakkyawan koyi da ya shafi sada zumunta, aminci, al’adun gargajiya da koyi da magabata.

A wannan hawa, matasan kan yi shiga irin ta masu sarauta (kamar sarki, hakimai,’yan lifidi da sauransu), dadin dadawa har da shiga irin wadda za ta kara hada kan mutanen Najeriya, kamar shigar ’yan kabilar Ibo da Yoruba da sauransu (ko don unguwar Faggen ta hada wadannan kabilu).

Abin dai gwanin sha’awa, domin duk ranar da ka riski kanka a unguwar a wannan lokacin, idan ma kai dan unguwar ne ko bako ne, za ka tarar kowa cikin farin ciki da annashuwa, kuma cikin kwanciyar hankali.

Kwatsam! Sai ga shi a dole an hana yin wannan hawa. Tabbas, jami’an tsaro suna da ikon hana hawan bisa wasu dalilai na tsaro da su suka fi kowa sani. Sai dai su ma matasa, kundin tsarin mulkin kasa ya ba su damar yin wannan zagayen, musamman idan za su yi shi cikin lumana (kamar yadda suka rika yi a baya).

A ganina, idan har wadannan jami’an tsaron suka yanke wannan hukuncin saboda sanin tsaro, to ya kamata a ce sun san yadda za su haifar da tsaro a yayin aiwatar da wannan zagaye na matasa idan suna tunanin wasu za su shigo cikin sha’anin su haifar da rashin tsaron.

Uwa uba ma, ya kamata su san cewa; Unguwar Fagge fa, unguwa ce ta ’yan uwan juna, shi ya sa ake kiranta Fagge Sodangi, yawanci wane surukin wane ne, wane dan uwan wane ne. Sannan a iya sanina, duk matashi ko matashiyar da aka ga ta fito yin wannan hawa, sai an san shi, an san daga layin da yake, sai ma mutum ya yi rijista.