Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da ranakun Juma`a 19 da Litinin 22 ga wannan wata na Afrilu a matsayin ranar hutu, domin baiwa kiristoci damar yin bikin Easter.
Ministan ma’aikata cikin gida na Najeriya Abdulrahaman Dambazau ya bayyana hakan, a wata sanarwa da Babban Sakatare na ma`aikatar Barista Georgina Ekeoma Ehuriah ya sanyawa hannu.
Minista Dambazau ya yi kira ga kiristoci da su yi amfanin da wannan dama wajen yin koyi da koyarwa yesu al-masihu na kaunar juna da zaman lafiya da kuma hadin kai.