Wani kwararre a fannin tsaro ya ce bidiyon yakin Syria na tun 2021 ne kungiyar Boko Haram ta yi amfani da shi wurin ikirarin cewa ta harbo jirgin yakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya.
Hugo Kaaman, a kasar Sweden yi fallasar ne bayan bidiyon da kungiyar ta fitar ranar Juma’a da ya nuna wani jirgin yaki ya fashe a sararin samaniya, tana ikirarin cewa na sojin Najeriya ne mayakanta suka harbo.
- Ya kashe abokinsa saboda musun shekarun haihuwa
- Kakakin kungiyar Yarabawa, Yinka Odumakin ya rasu
- Tafsirin Ramadan: Izala ta tura malamai 500 zuwa kasashe
- Mu muka harbo jirgin yakin Najeriya —Boko Haram
A bidiyon, bayan fashewar jirgin, an ga wasu mayaka a kan ababen hawa a wani wuri mai kura, daga baya sai aka nuno wani mayaki dauke da bindiga a kan mushen wani jirgi mai dauke da alamar tutar Najeriya.
“An turo jirgin yaki na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya mai lamba 475 zuwa Sambisa ya yaki Mujahidai,” inji mayakin, fuskarsa a lullube.
An kuma nuna lambar jirgin Rundunar da ake nema da wata gawa da kungiyar ta ce na daya daga cikin matukan jirgin ne, yayin da wasu mayaka ke kwasar wasu abubuwa daga cikin jirgin da na matukin.
Amman tun tun bayan bullar bidiyon, kwararru a fannin ke tababar sahihancinsa, da cewa nisan da jirgin ke yi a sararin samaniya ya wuci inda kungiyar za ta iya harbo shi.
Da yake fashin baki a kan bidiyon, Kaaman ya ce jirgin da aka gani ya tarwatse a sararin samaniya, helikwaftan sojin Syria mai lamba SyAAF da aka harbo a 2012.
“Boko Haram ta fitar da bidiyon cewa jirgin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ne ta harbo.
“A bidiyon za a ga kamar jirgin ya tarwatse ne a sama, amma ba abin da ya faru ba ke na. Boko Haram ta yi amfani ne da bidiyon da aka dauka a 2012 na wani helikwafta SyAAP da ya tarwatse a sararin samaniya a Idlib ta yi masa saddabaru,” inji shi.
Kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), Edward Gabkwet, ya ce Boko Haram ba ta da karfin harbo irin jirgin, kuma bidiyon na bogi ne.
“Duk da cewa ana kan nazarin bidiyon, a fili yake cewa yawancin bangarorin bidiyon an yi saddabarun su ne ta yadda za su nuna harbo jirgin aka yi.
“A bayyane yake cewa yadda Boko Haram ta saba farfaganda, tana so ne ta fake da hatsarin jirgin da dalilan faruwarsa na da yawa, ta nuna cewa ita ta harbo shi; a lokacin da sojoji Najeriya suka riga suka gurgunta ta,” inji sanarwar da ya fita.
Shi ma masanin tsaro, Abubakar Ismail, bayan ya kalli bidiyon ya ce, “Iya harbo jirgin sama sai da kwarewa da kuma makami mai linzami tunda ba helikwafta ba ne. Amma ganin yadda jirgin ya fashe a sama ya nuna akwai wata matsala.”
A ranar Alhamis ce NAF ta sanar cewa tana neman jirgin yakinta mai lamab NAF 475, wnada sadarwa ya katse tsakaninta da shi a yayin da yake mara wa dakarun kasa baya a yaki da Boko Haram a Jihar Borno a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce a yayin da ake neman jirgin da kokarin ceto matukansa, ba za a iya cewa ga hakikakin abin da ya faru da shi ba, duk da cewa komai na iya faruwa.
Washegari ne Boko Haram ta fito da bidiyon nata wanda a ciki take ikirarin cewa mayakanta ne suka kakkabo shi.
Amma Hugo Kaaman ya ce, “Tabbas jirgin ya fado kamar yadda aka ga mushensa a cikin bidiyon, amma babu tabbacin matsala ya samu, ko kuma makiya ne suka harbo shi.
“Bidiyon ya nuna karya Boko Haram ta ke yi da bidiyon,” inji shi.