✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bidiyon Dala: Na koma Burtaniya har sai kura ta lafa – Jaafar Jaafar

Jaafar ya ce ya koma Burtaniyar ne kuma ba zai dawo ba har sai kura ta lafa in ya sami tabbacin kiyaye rayuwarsa.

Mawallafin jaridar nan ta intanet mai suna Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ya ce ya shi da iyalansa sun koma kasar Burtaniya bayan barazanar da ake yi wa rayuwarsu.

Jaafar, a yayin wata tattaunawa ta wayar salula ya ce ya koma Burtaniyar ne kuma ba zai dawo ba har sai kura ta lafa in ya sami tabbacin kiyaye rayuwarsa.

“Zan ci gaba da zama a nan har sai na sami natsuwar cewa idan na dawo wannan gwamnatin za ta iya kare rayuwata da kuma tabbatar da ’yan cin ’yan jarida,” inji shi.

A watan Oktoban 2018 ne dai Jaafar din ta jaridarsa ta Daily Nigerian ya wallafa wasu faya-fayan bidiyo wadanda a cikinsu aka ga Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yana saka Dalolin Amurka a aljihu, wadanda ake zargin na cin hanci ne daga dan kwangila.

Bidiyon dai ya bata sunan Gwamnan matuka, ko da yake bai hana shi sake lashe zaben Gwamna a 2019 ba.

To sai dai Jaafar ya dada shiga tsaka mai wuya ne a ‘yan kwanakin nan bayan an jiyo Gandujen a cikin wani shiri mai suna ‘A fada a cika’ na BBC Hausa yana cewa bidiyon karya ne kuma nan ba da jimawa ba za su hukunta wadanda ke da hannu a cikinsa.