Mawallafin jaridar nan ta intanet mai suna Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ya ce ya shi da iyalansa sun koma kasar Burtaniya bayan barazanar da ake yi wa rayuwarsu.
Jaafar, a yayin wata tattaunawa ta wayar salula ya ce ya koma Burtaniyar ne kuma ba zai dawo ba har sai kura ta lafa in ya sami tabbacin kiyaye rayuwarsa.
- ’Yan bindiga sun yi barazanar kashe ragowar daliban Jami’ar Greenfield da suka sace
- An mayar da ’yan Arewa 42 gida daga Ondo
“Zan ci gaba da zama a nan har sai na sami natsuwar cewa idan na dawo wannan gwamnatin za ta iya kare rayuwata da kuma tabbatar da ’yan cin ’yan jarida,” inji shi.
A watan Oktoban 2018 ne dai Jaafar din ta jaridarsa ta Daily Nigerian ya wallafa wasu faya-fayan bidiyo wadanda a cikinsu aka ga Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yana saka Dalolin Amurka a aljihu, wadanda ake zargin na cin hanci ne daga dan kwangila.
Bidiyon dai ya bata sunan Gwamnan matuka, ko da yake bai hana shi sake lashe zaben Gwamna a 2019 ba.
To sai dai Jaafar ya dada shiga tsaka mai wuya ne a ‘yan kwanakin nan bayan an jiyo Gandujen a cikin wani shiri mai suna ‘A fada a cika’ na BBC Hausa yana cewa bidiyon karya ne kuma nan ba da jimawa ba za su hukunta wadanda ke da hannu a cikinsa.