Kwanaki 30 bayan Babbar Kotun Jihar Kano ta umarci Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya biya mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar tarar N800,000, mawallafin ya ce har yanzu ba a biya shi kudin ba.
A ranar Talata, shida ga watan Yulin 2021 ne dai kotun ta umarci Gwamnan ya biya Jaafar kudin a matsayin tara bayan ya janye tuhumar da yake masa kan bata suna ba tare da wata kwakkwarar hujja ba kan karar da yake da shi.
Tun da farko dai Ganduje ya gurfanar da mawallafin jaridar ne a gaban kotu kan wasu faya-fayan bidiyo da jaridar ta wallafa inda suka nuna Gwamnan yana karbar Daloli da ake zargin na cin hanci ne yana zuba wa a aljihu.
Kotun, a karkashin jagorancin Mai Shari’a Suleiman Danmallam wacce ta amince da bukatar Gwamnan ta janye karar ta umarce shi da ya biya Jaafar din da jaridarsa ta Daily Nigerian tarar N400,000 kowannensu.
To sai dai Jaafar ya tabbatar wa wakilin Aminiya cewa har yanzu Gwamnan bai bi umarnin kotun ba bayan kwana 30.
Ya ce har yanzu ba a tuntube shi ko kuma lauyansa ba a kan lamarin.
Aminiya ta rawaito cewa a watan Oktoban 2018 ne Daily Nigerian ta wallafa bidiyoyin da suka nuna Gwamnan na karbar Dalolin da ta yi zargin na toshiyar baki ne, ko da yake Ganduje ya sha musanta wa inda ya ce an tsara su ne don a bata masa suna.