Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sake maka mawallafin jaridar intanet ta DAILY NIGERIAN, Jafar Jafar a kotu.
A watan Oktoban 2018 ne dan jaridar ya saki wasu bidiyo na zargin Gwamnan Kanon da karbar rashawa a hannun wasu ’yan kwangila a jihar.
- ’Yan bindiga sun kashe Janar din soja, sun sace matarsa
- Masu juna biyu sun mutu wajen rububin karbar abinci a Borno
Lamarin da ya tada kura a sassan Najeriya ya sa gwamnan maka Jafar a kotu don ta bi masa kadinsa kan abin da ya kira cin mutunci da bata suna.
Bayan daukar lokaci ana shari’a, gwamnan ya janye karar da ya shigar, inda a ranar 6 ga watan Yuli, 2021 kotun ta umarce shi ya biya dan jaridar N800,000 saboda bata masa lokaci da ya yi.
Sai dai a ranar 15 ga Yuli, 2021 Ganduje ya sake maka Jafar a wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja.
An aike wa dan jaridar takardar sammaci ana bukatar ya bayyana a gaban kotun cikin makonni biyu masu zuwa.
A baya, Jafar Jafar, ya maka Ganduje a kotu yana neman a biya shi N3,000,000 kan barazana da bata suna da Gwamnatin Kano ta yi masa.