Dan jaridar nan da ya fitar da bidiyon zargin Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano da karbar daloli a matsayin cin hanci, Jaafar Jaafar ya hadu gwamnan a kasar waje.
A ranar Litinin Jaafar Jaafar, mawallafin jaridar Daily Nigerian, ya wallafa bidiyon haduwarsu da Ganduje a birnin London na kasar Birtaniya.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Dawo Aiki
- Jiragen yaki sun hallaka ‘yan ta’adda 7 da ake nema ruwa a jallo a Kaduna
Duk da takaddamar da ke tsakaninsu, a karon farko, a bidiyon, an ga Gwamnan Ganduje da Jaafar Jaafar kowannensu cikin sakin fuska da raha, suka sha hannu, sannan suka rungume juna.
Hakan ta kasance ne a harabar Chatham House, inda dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya je gabatar da jawabi a ranar.
Ganduje wanda dan ga-ni-kashe-nin Tinubu ne, yana cikin manyan ’yan Jam’iyyar APC da suka raka dan takarar zuwa Chatham House, inda a nan suka sake haduwa da dan jaridar.
Dambarwar bidiyon Dala
A shekarar 2018, kafofin Daily Nigerian mallakar Jaafar Jaafar suka fitar da wani bidiyo — da ya tarar da kura — wanda a ciki aka ga wani wanda dan jaridar ya ce Ganduje ne, yana karbar daloli yana cusawa a aljihu.
Dan jaridar ya yi zargin cewa gwamnan ne a bidiyon a lokacin da yake karbar cin hanci a kudin Dalar Amurka daga wani dan kwangila da Gwamnatin Jihar Kano ta ba wa aiki — zargin da gwamnan ya sha karyatawa.
Daga bisani Ganduje, wanda ya ce an yi wa bidiyon suddabaru ne, ya maka Jaafar Jaafar a kotu, yana neman diyyar Naira biliyan uku kan zargin bata masa suna.
Gwamnan ya kuma ce ya kafa kwamiti domin gudanar da bincike kan bidiyon da masu hannu a ciki.
Har yanzu shari’ar na gaban kotu, a yayin da Jaafar ya koma kasa waje, tare da cewa ana yi wa rayuwarsa barazana kan bidiyon da ya fitar.