Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano zamanin mulkin Dr Abdullahi Umar Ganduje, Malam Muhammad Garba ya ce batun Bidiyon Dala ba zai hana maigidansa samun muƙami ba.
Muhammad Garba ya bayyana hakan ne a ra’ayinsa da aka wallafa a jaridu inda yake yaba cancantar Ganduje na zama minista ko shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.
Tsohon kwamishinan ya ce rahotannin da ake yaɗawa cewa an samu tsaikon naɗa ministoci ne saboda shugaban ƙasa Bola Tinubu na son janye sunan Ganduje domin naɗa shi shugaban APC na ƙasa na tabbatar da matsayin Gandujen a siyasar Najeriya.
Zaɓin Ganduje lalata tsarin APC ne – Salihu Lukman
Ganduje zai zama shugaban APC na ƙasa
Bayan da ya bada tarihin gwagwarmayar siyasa, aiki, mulki da karatun Boko na gwamna Ganduje, Muhammad Garba ya kuma karkata alƙaminsa kan waɗanda ya kira ‘yan adawa masu neman ɓata masa suna.
Ya ce “mutanen da ake zargi da wannan ɓata sunan, musamman dawo da tsohuwar maganar Bidiyon Dala, sun yi haka a 2019 domin hana Dr. Ganduje zama ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC.
“Sai dai sun yi faɗuwar baƙar tasa a wancan lokacin kuma yanzu ma suna ci gaba da maganar ne saboda dalilai na siyasa.
“Kamar yadda na faɗa a baya, waɗansu daga cikin mutanen sun yi wa takarar shugaba Tinubu zagon ƙasa tare da faɗin maganganu a kansa kafin ya zama shugaban ƙasa.”
Don haka tsohon kwamishinan ya ce ya na da yaƙinini matsayin Dr Ganduje a wurin shugaba Tinubu ya kai yadda babu yadda za’a yi a hana shi zama ko dai minista ko kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.