Shugaban Amurka Joe Biden, ya kammala ziyarar aiki da ya soma tun makon jiya a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wannan ziyara ta kwanaki hudu da Biden ya kai Gabas a Tsakiya, ita ce irinta ta farko tun bayan dare wa madafun iko watanni 18 da suka gabata.
- Dimokuradiyya ce ta yi tasiri a zaben Osun —Buhari
- Mutumin da ya auri jikarsa a Zamfara ya ki rabuwa da ita
Biden ya karkare ziyarar ce da halartar taron koli na Majalisar Kawancen Hadin Kai na kasashen yankin Gulf mai mambobin shida.
A taron wanda kuma kasashen Masar da Jordan da Iran da suka halarta, Biden ya jaddada matsayar Amurka na ci gaba da zama babbar kawa ga kasashen yankin.
Mahukunta a Isra’ila na fatan wannan ganawa da shugaba Biden ya yi da shugabannin kasashen ya taimaka wajen samar da kungiyar kawancen tsaro da ita ma za a saka ta a ciki, a wani mataki na kara hadin kai domin tunkarar barazanar da kasar Iran ke da shi ga yankin.
A ganawar da ya yi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, Joe Biden ya tabo batun mutunta ’yancin dan adam, da batun tsagaita wuta a kasar Yemen gami da batun kisan dan jaridar nan, Jamal Khashoggi.