Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na China Xi Jinping, sun gana ido da ido a tsibirin Bali na kasar Indonesiya, gabanin Babban Taron Koli na kasashe masu karfin tattalin arziki.
Shugabanin kasashe masu karfin tattalin arziki da dama sun isa tsibirin Bali da ke kasar Indonesiya don halatar taron koli na G20.
- Kotu ta soke zaben dan takarar gwamnan APC a Akwa Ibom
- Ta’addanci: Kotu ta dage shari’ar Kanu sai abin da hali ya yi
Bayanai sun ce tuni Shugaba Joe Biden na Amurka da takwaransa na China, Xi Jinping suka yi wata ganawa, wacce ita ce ta farko ta keke da keke tun bayan da Biden ya hau karagar mulki.
Ana sa ran za su yi kokarin dinke barakar da ke tsakaninsu a yayin wannan ganawar da suka yi a gefen taron na G20 a wannan Litinin.
A hukumance daga gobe Talata za a soma taron kuma halin da duniya ta tsinci kai na tashin farashin kayayyaki da tsadar makamashi a sakamakon yakin Rasha da Ukraine, za su kasance daga cikin manyan batutuwan da shugabanin za su tattauna a taron.
Babu alama Shugaba Vladimir Putin na Rasha zai halarci taron a sakamakon yadda aka mayar da kasar saniyar ware saboda mamayar Ukraine.