✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bene mai hawa 21 ya danne mutane da dama a Legas

Yanzu haka ma’aikatan kwana-kwana na ta kokarin ceto mutane.

Wani dogon bene mai hawa 21 ya rushe tare da danne mutane da dama a unguwar Ikoyin Jihar Lagos.

Benen, wanda ake tsaka da gina shi na kan titin Gerald ne a unguwar ta Ikoyi.

A yanzu haka dai ma’aikatan kwana-kwana daga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na Kasa (NEMA) tare da na Jihar Legas (LASEMA) da jami’an kwana-kwana suna wurin domin aikin ceto wadanda ginin ya danne.

Darakatan hukumar LASEMA Femi Oke-Osanyintolu yace sun kai daukin ne bayan kiran gaggawa da aka yi wa hukumar waya daga inda lamarin ya faru.