✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bellerin ba zai sake buga wasa a bana ba saboda rauni – Arsenal

Kulob din Arsenal da ke Ingila ya fadi a ranar Talatar da ta wuce cewa dan kwallon bayanta Hector Bellerin ba zai sake buga wa…

Kulob din Arsenal da ke Ingila ya fadi a ranar Talatar da ta wuce cewa dan kwallon bayanta Hector Bellerin ba zai sake buga wa kulob din wasa a bana ba saboda mummunan raunin da ya samu a kokon gwiwarsa ta dama.

Bellerin, mai shekara 23, ya samu raunin ne a wasan da kulob din ya yi da na Chelsea a gasar rukunin Firimiya na Ingila a ranar Asabar da ta wuce.

Dan kwallon ya samu raunin ne a minti na 72 da fara wasa wanda hakan ya sa kocinsu Unai Emery ya canja shi da Mohammed Elneny dan Masar.

Bayan likitoci sun yi bincike a kan Bellerin ne suka gano dan kwallon ba zai iya buga kwallo a kakar wasa ta bana ba saboda munin raunin.

Jaridar The Guardian ta Ingila ta ce idan ba a yi hankali ba, da kyar ma dan kwallon ya murmure kafin a fara kakar wasa mai zuwa a watan Agustan bana.

A wasan Arsenal ce ta lallasa kulob din Chelsea da ci 2-0 wanda hakan ya sa har yanzu take matsayi na 5 a teburin gasar.

Don haka dan kwallon ba ya cikin wadanda za su kara da kulob din Manchester United a gasar cin Kofin Kalubale (FA) da za a yi a yau.