✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Belin-auta ko billen-wauta?

Yan makarantarmu da suka kware a fannin tsimi da tanadi, wajen tsimin dukiya da riritata, na tabbatar za ku bijiro wa Gwamnatin tarairayar Haurobiyawa tambayoyi…

Yan makarantarmu da suka kware a fannin tsimi da tanadi, wajen tsimin dukiya da riritata, na tabbatar za ku bijiro wa Gwamnatin tarairayar Haurobiyawa tambayoyi game da shirinta na jinka wa jihohi damin Hauro gashin balama kaza da kaza (ba fa tsuntsun miya ba), don biyan ladar kwadago da sauran ayyukan raya kasa. Abin da ya sa na ari bakinku na ci muku albasa mai lawashi, shi ne, ganin cewa, tsohon Gwamna mai Kwarankwatsin tsiya na birnin Dabo, wanda a yanzu Sani-atta ne, ya yi wa magajinsa Mai dillaro aiki a gandun daji watsattsaken wasika, don nuna adawarsa da neman kudin beli har Hauro malala gashin tunkiya tsayuwa bisa kafa guda da zagaye. Can ma a birnin Dikko, wato Jihar dakin-kara an kwata irin wannan, inda Gwamna Mai sare-sare, ya bukaci a saro masa dami. Kai har a Jihar Jijjiga ciyawa ana yunkurin karbo damin Hauro, a matsayin belin ceton tattalin arziki, ta yadda Gwamna Bandirawo zai kwata shatale-talen Turaklin Hawan-sa, wanda aka ce ya rika mulkin jihar ta hanyar bayar da umarni a akwatunan sakon na’ura mai kwakwalwa, har ta kai ga maroka na yi masa kirari da Gwamna mai kwamfuta ko kwanon-fita.

Tun kafin mu lula cikin wannan darasi, ina ganin gara Farfajiyar Dodorido mahayin shorido ta fayyace wa masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafa cewa, idan muka bari aka ceto lalitar gwamnatin jihohi, har suka cicciko, to belin auta yana iya karkewa da zama belin cuta ko billen wauta. Wadanda suka kasa fasko abin da nike kokarin nusar da mu, sai su kalli masu murguda baki kamar sun ci kilishi, sun kan ga gilashi, suna ta yaren Ingilishi, a nan za su fasko yadda ake furta belin auta ko billen wauta.
Haurobiyawa, idan ba mu kakaba wa kurungunmu tagiyar Malam Mantau ba, kowa zai iya tuna yadda muka yi darasi kan tsimi da ta’adi, har muka ce wa Gwamnatin Haurobiya ta zamanin da, ga lukudi, ga lakume kudi; mun kuma taba gabatar da darasi mai taken: Kanwar kudi: sinadarin buga Hauro, inda ’yan wala-wala suka dama wa al’umma furar yawon-dara. Kai har masu ayyukan tsayuwa bisa kafa daya da sili da manuniyar kasa mun bijiro da aika-aikarsu. ’yan makarantarmu na da labarin Kwamandan kalallame Hauro; da Turmin dakan Hauro, wadanda suka haure da ’yan matsabban Haurobiyawa.
Batu na ingarman karfen karafa, a matsayina na katafarten direban alli a cikin Amintacciyar Jaridar kasar Haurobiya, nakan bijiro da irin wadannan darussa ne domin kada miyagu su cutar da al’umma, tunda nasan ’yan damun-fura da yawon-dara sun cika gari, don cimma manufarsu ta jefa al’umma cikin garari.
Abin da kawai nike son nusar da mu shi ne, kada Gwamnatin Tarayyar Haurobiyawa ta jinka wa jihohi damin Hauro, su kuwa, su jefa al’ummarsu cikin haure-haure da hauragiya. Saboda haka mu kakaba wa kurungunmu tagiyar Malam Tunau, don fasko yadda tsohon Gwamna Turakin Hawan-sa na Jihar Jijjiga ciyawa ya yi wa duniya shataletale da dukiyar al’umma; shi ma magajinjsa tsohon Gwamna mai sunan sulalla, ya sulale tun kafimn talgen tuwo ya sulala. Sannan Shayin-mama ya shammaci al’umma a birnin Dikko duk da cewa ya barko ayyuka, tare da aika-aika. Shi kuwa tsohon Gwamna Mai kwarankwatsin-tsiya na birnin Dabo, hakika ya kwankwatsa aiki, amma a cikin birni kawai, inda aka yasar da mutanen karkara har an kusa yi musu kakara da kara.
Lallai akwai bukatar a fayyace wa Haurobiyawa abin da ake son yin da kudin beli, indai ba wanzami za a jinka wa don tsige wa jarirai beli-beli ko billen shafaffu da mai. Kun ga ke nan akwai bukatar Gwamnatuin Tarairayar Haurobiyawa ta kwararo bayani kan yadda take son a kyautata rayuwar al’umma a daukacin jihohin Haurobiya. Sannan kowane Gwmana gwarangwam ya jajice don ganin bai jefa muitanensa cikin jangwam ba.
Kuma ga Asusun ’yan koko ya taba tallata Gwamnatin Jihar Zaman-fara, ibnda ta bayyana cewa, sun gurfanar da mahukuntan birnin Gusun da birnin Shehu, don su biya kokon su da aka kwankwada. Ko yaya suka karke, ni ba ni da masaniya, illa dai kawai su ma mahukuntan sun tallata cewa, sun dauri aniyar biyan kokon da suka kwankwada daga wannan asusun. Shin talakawa ne suka kwankwadi kokon ko kuwa jiga-jiga gwamnati tare da Gwamna gwarangwam ne suka jefa jama’a cikin jangwam.
Haurobiyawa a taka kahan-kadaran, domin a daidai lokacin da na karkare wannan darasi, batutuwa sun cika kasar nan kan cewa. Baban masu Burin-huriyya ya ingiza keyar Loma-a-murde, ya kuma maye gurbinsa da wani Iron mugun madambaci, da ya kware wajen hana magu-magu. Don haka wanda duk ya salwantar da matsabban al’umma, ko ya dama musu furar yawion-dara, hakika za a kada masa jauje a kudarsa.
Anan ina kira da uwa mabada mama, wato Gwamnatin Tarairayar Haurobiyawa, duk jaririn da ta shayar da shi, idan ya zubar da kokonsa ko madarar da aka difara masa, to kada a sake zuba masa wata, har sai ya natsu. Wannan doka ina so ta yi aiki har akan Jinjinido da Jarirido (Jaririn-dodo da Jinjinniyar-dodorido), ta yadda ba za mu yi belin-auta da zai zama billen wauta ba. Mu himmatu wajen aiwatar da tsarin tsimi da tanadi don kasha karsashin asara, har mu haifar da riba. Duk wanda aka kama yana wadaka da fantamawa a damin dukiyar Haurobiyawa sai ku hada shi da sabon shugaban hukumar Gogarma mai arangama da gwagwarmaya da masu fashi da mukami ko da dabara.
…Dubu karamin lauje ko kauje
Haurobiyawa, duk da cewa ni ba dan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ba ne ba, hasalima mun yi artabu da tsawon shekaru sili da manuniyar sama da suka shafe suna mulki, ban goyi bayan jinka wa matasan da ke zaman kasha fatari da buje Hauro dubu karamin lauje ba. Domin tsarin ba mai dorewa ba ne.
Abin da ya dace ayi, shi ne, duk wanda ya iya fardar gayauna da kiwon tsuntsaye da bisashe, to a jinka masa wadannan matsabbbai tare da kayan sana’a na tsawon rabin shekara. Daga nan sai a ce kowa ya iya da kansa. Don gudun kada a samu dimbin masu zaman dirshan, suna jiran a jinko musu ’yan matsabbai, sai a kara kaimin cusa sana’o’i a manhajar makarantu, manya da kananan. Uwa-uba a nusar da masu bobo da kwambon bokoko cewa ba lallai sai mutum ya yi kwadagon farar kwala ba. Ana yakar juhala ne, don tabbatar da adala. Saboda a a koyi watsattsake da buda wagagen littattafai da zimmar farde gayauna ko limbu-limbu a cikin lambu ko sake-sake da ’yan dinke-dinke.
Hauyrobiyawa, musamman masu koyon watsattsake da buda wgagen littattafai a Amintacciyar Jaridar kasar Haurobiya, mu nusar da ’yan dugwi-dugwi da matasa masu fuka-fukin tashi, muhimmancin neman na kai yadda Japanawa da Koriyawa da Malesiyawa da mutanen gidan-Indon-siya ke yi, don kauce wa zaman kashe fatari. Da fatan kowa ya gane, har ma da ’yan bayan kango, yaran Gizo-gizon-dakin-gwaggo.
Jam’iyyar Baban Burin-huriyya, mai maganin zogi da radadin ciwon kurungu, ina fatan za ku dabbaka manhajar makarantu, tunda kowa ya san babu hajijiya a cikinta.