Babbar Kotun Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano ta sanya 31 ga watan Maris, 2022 a matsayin ranar yanke hukunci a kan bukatar ba da belin Sheikh Abduljabbar Kabara da lauyansa ya gabatar mata.
Ana zargin Abduljabbar Kabara ne dai da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma tayar da hankalin jama’a.
Sai dai lauyoyin masu shigar da kara karkashin jagorancin Barista Saida Suraj sun nemi kotu ta yi watsi da bukatar bisa la’akari da girman laifin da ake tuhumar wanda ake zargi, wanda a cewarsu zai iya kai ga yanke mishi hukuncin kisa, karkashin dokar Kundin laifufuka ta Jihar Kano ACJL 171 (1).
Hakan ya sa alkalin kotun, Mai Shari’a Sani Sarki Yola ya dage zaman da mako biyu, zuwa ranar 31 ga watan Maris don jin ra’ayin kotun game da batun bayar da belin.