Amsoshin tambayoyin masu karatu
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikin sa, amin. Insha Allah za mu kammala bayani kan dabarun zama da mata sama da biyu, sannan mu kawo wasu daga cikin tambayoyin masu karatu. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfani dukkan masu bukatarsa, amin.
Ya kamata maigida ya kasance kodayaushe yana cikin rokon Allah Ya sanya ya zama mai adalci da kyautata wa matansa, mai kare musu dukkan hakkokinsu, da kuma rokon Allah Ya kara hada kansu kuma Ya albarkaci zamansu. Ya sa ya zama hanyar da za ta kai su aljanna. A lokacin sujada maigida ya kasance yana neman taimakon Allah a kan hakan, haka ma a lokacin yin kowace addu’a, to maigida ya rika sako wannan addu’a a ciki.
karfin Mijintaka:
Dabara ta 4: Halartacciyar karya,
Wata sa’in ko yaya maigida ya dage wajen tsayar da adalci da kyautatawa tsakanin matansa; to wata rana sai sun so kure shi saboda ajizanci irin na ‘ya mace, don haka ba laifi sarko halartacciya karya nan da can, don ganin cewa kodayaushe zama tsakaninka da su yana tafiya cikin taushi da kwanciyar hankali. Maigida zai iya amfani da halartacciyar karya a wadannan wuraren:
• Kamar wajen yabo da koda matansa, babu laifi don ya dan kara wa zuma zaki, domin kalami mai dadi yana da matukar tasiri ga jin dadin zuciyar ‘ya mace, amma sai dai a kula kar a yabi daya da wasu kalamai masu dadi kuma aje abyi wa daya daidai irinsu ba ragi ba kari, sai dai a dan caccanza, kai kanka sai ya fi maka dadi in ka dan canza din, kowacce a yabe ta da abin da ya dace da ita, kuma abin da aka san zai yi matukar yi mata dadi a rai in ta ji shi. Wasu mazan kan yi kuskuren aikawa da sakon tes iri daya ga matansu, karshe kuma matan su zo su gane hakan, wannan ba zai taba sa masu dadin rai ba, don kowace mace tana son a yi mata yabo na musamman daban da na wata macen.
• Wasu matan suna da jarabin son su ji maigidansu ya ce su ne mowa, ko su ya fi jin dadin ibadar aure da su, to a nan in wata daga cikin mata ta dage da nacin son jin wannan, nan ma maigida na iya yi mata wannan karyar, don dai ya kashe wutar jarabin nata. In ma su duka ne suka dame shi da irin wannan tambayar, kowacce sai ya gaya mata abin da take son ji.
• Maigida zai iya yin karya idan ya gane karya ce za ta cece shi wajen wanzar da zaman lafiya. Halartacciyar karya ana yinta ne kadai don dadada wa mata, ba don shi maigida ya dadada wa kansa ba, don haka ba a karya don cutarwa ga wata ko don danne wa wata hakkinta, kuma kada a bari ta yi yawa.
karfin Mazantaka:
A yanayi irin na zama da mata sama da daya, dole sai maigida ya yi amfani da dukkan karfin mazantakarsa don ganin an yi zaman lafiya na ba cuta ba cutarwa; domin Allah Ya hore wa mata kambin baka, ta yadda za su mai da fari ya zama baki cikin sauki, da iya kulla makirci; don haka sai maigida ya yi amfani da kaifin basira da hangen nesa don gane gaskiyar kowane irin al’amari lokacin da yake faruwa ko bayan ya faru. Sannan da karfin mazantakarsa ne zai kafa dokokin da za su tabbatar da zaman lafiya tsakanin matansa. Haka da karfin mazantakarsa ne zai tilasta matansa yin abubuwan da suka dace na addini da na yanayin zamantakewa. Kada maigida ya zama mai sanyi-sanyi game da iyalinsa, duk abin da suka ga dama su yi kawai, ko ya zama yana shakkarsu don haka ba ya iya matsa masu do su aikata abin da yake daidai. Haka kuma yana daga cikin karfi mazantaka miji ya kasance mai ji da matansa, ya shagwaba su. Amma ba karfin mazantaka ba ne maigida ya takura wa matansa sosai har ya zama suna tsananin tsoronsa, karfin mazantaka shi ne tsaka-tsakin wannan. Kuma yana daga cikin karfin mazantaka iya hukunta duk wacce ta saba doka ta hanyoyin da shari’a ta aza na a hukunta matar da ta fandare.
Tambayoyinku:
Ba ya daraja iyayena!
“Assalamu Alaikum, Don Allah ki taimaka ki amsa min tambayata cikin gaggawa, saboda halayen maigidana sun ishe ni, gab nake da in bar gidansa! Domin ba ya ganin girman mahaifana da ‘yan uwana baki daya, kuma sai ya rika ikirarin shi mai kaunata ne, mu biyu ne amma ita dayar ba haka yake mata ba. Shin yana daga cikin hakkokin aure ga ma’aurata su girmama iyayen junansu? Gimbiya A.”
Wa alaykumus salam, tabbas yana daga cikin hakkokin aure ma’aurata su girmama iyayen junansu, ba ya halatta ga daya ya wulakanta iyayen daya a bisa kowane irin dalili ne ma. A shari’ance, Musulmin da ba a san shi ba ma, yana da hakki na a kyautata hulda da shi, kuma cin zarafin Musulmi yana daga cikin abubuwan kyama da Annabi SAW yayi tir da su, to balle kuma Musulmin da surukuntaka ta hada? Tozarta ko wulakanta surukai ba daidai ba ne, kuma ya saba wa shari’a, ko da kuwa su surukan ne ke yin abin da ke zubar musu da daraja, ba za a wulakanta su ba sai dai a yi musu nasiha da addu’a, kuma a ci gaba da hakurin zama da su. Ba daidai ba ne ki bar gidan mijinki a kan wannan dalili kadai, domin matsala ce da a zama daya ma ana iya kawo maganinta, iyaka sai ki kai kararsa ga magabata ko wani wanda kika san zai yi masa nasiha ya yi aiki da ita, in duk kin yi iya yin abin ya ci tura, to sai ki ci gaba da hakuri da addu’a, ki yi zamanki a gidan aurenki. Kuma ki sa a rika taya ki da addu’a Allah Ya yaye masa wannan rauni, Ya datar da shi ga aikata abin da shi ne ya dace da shari’a da zamantakewa. Kuma sai ku zauna ku yi shawara ke da iyayenki da ‘yan’uwanki, in ta kama ma, to su kaurace yin zumunci da maigidan naki, ko duk wani abu da kuka ga shi ne mafita. Amma ban da maganar kashe aure, in an yi haka wani kuskuren ne za a daba a kan wani; in kin fita kika san abun da ke jiranki can wajen auren? Kika san ko Allah Ya jarabce ki da wani abu ma da ya fi haka? Ki sani wasu suna fuskantar abin da ya fi wannan a gidan aurensu, amma sun ci gaba da hakuri, don haka ke ma ki ci gaba da hakuri, komai ya yi farko, to zai yi karshe.
Na yi zagi a gaban danmuAssalam alaikum,
Na yi kuskure malama- cikin zafin rai na gaya wa matata kalma mai kamar zagi a gaban danmu (mai wayau) sai ta fara kuka, nan take na yi nadama, na ba ta hakuri na nemi ta yafe min, ta hakura kuma ta yafe min. Ya ya zan yi dan namu ya manta kuma ya daina kallona da abin da na yi wa mahaifiyarsa? Kuma kada ya tashi da muguwar dabi’a irin wannan? Ina cikin damuwa sosai, don Allah a ba ni shawara.
Nagode, A N Rogo.
Wa alaikumus salam,
Abin yi sai ka zaunar da shi, ka nuna masa abin da ya ga ka yi din nan kuskure ne, da yakan zo daga shaydan. Ka nuna masa yin haka ba abu ne mai kyau, kuma ka gargade shi da kada wata rana ya ce zai yi irin haka.
Ka kyauta da wannan tunani da ka yi, lallai da yawa iyayen wannan zamani ba su damu wajen koyar da ‘ya’yansu munanan dabi’o’i da ba za su kare su da komai ba sai wahala da bakinciki.
Shin Ya Halatta?
Assalamu alaikum, ina tambaya ne a kan raba daidan lokaci tsakanin matan mutum: Ni shagona ya kasance a gidan dayan matata, to idan ba ranar aikinta ba ne ya halatta in shiga gidanta in ci abinci ko wata lalura?
Wa alaikumus salam, babu laifi shiga don cin abinci ko wata lalura, amma da sharadin ba za ka tsaya yin hirar annashuwa da ita ba, sai dai maganar da ta zama dole, kuma abincin ya kasance na waccan mai aiki ne ake kawo maka, ko kuma ita ce ta amince a kan wannan ta rika ba ka abincin tun da ta fi kusa.